Home Back

Abincin da za ku bai wa yaranku don kauce wa kamuwa da tamowa

bbc.com 2024/7/3
..

Asalin hoton, Instagram/ Humaira's Varjeties

  • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • Twitter, @bellodiginza
  • Aiko rahoto daga Abuja

A makon da muke ciki ne ƙungiyar Likitoci ta Duniya, Medicine San Frontiers (MSF) ta fitar da rahoton da ta saba fitarwa na rubu'in farko a shekarar 2024.

Rahoron ya nuna cewa an samu ƙaruwar yaran da ke fama da matsalar cutar tamowa - da rashin wadataccen abinci mai gina jiki ke haddasawa - a arewacin ƙasar.

Rahoton ya ce jihohin Borno da Bauchi da Zamfara da Kano da Kebbi da Sokoto na daga cikin jihohin da aka samu ƙaruwar yaran da ke fama da cutar.

MSF ta ce akwai buƙatar ƙara wayar da kan jama'a da haɗa ƙarfi wuri guda domin kawar da wannan matsala da ma cutuka da dama.

Ana dai alaƙanta ƙaruwar matsalar da rashin tsaro da yankin arewacin ƙasar ke fuskanta, lamarin da ya sa manoman yankin ba su samun damar yin noma.

Galibi dai rashin abinci mai gina jiki ne ke haddasa kamuwa da cutar.

Nau'in abincin da jiki ke buƙata don kauce wa tamowa

Dakta Auwal Musa Umar, ƙwararren likitan Cimaka kuma shugaban ƙungiyar Likitocin Abinci reshen jihar Kano ya kuma yi bayanin abinci da ya kamata a bai wa yara domin kauce wa kamuwa da cutar tamowa.

Ya ce jikin yara na buƙatar duka nau'ikan rukunin abinci da ake da su, kamar masu ƙara kuzari da mai gina jiki wanda shi ake buƙata sosai wajen gina garkuwar jiki.

Sai kuma nau'in abinci mai ɗauke da sinadarin vitamins da masu bayar da kariya.

''A ƙa'ida ana son yaro ya samu duka waɗannan nau'ika a abincinsa idan ana so ya kauce wa kamuwa da tamowa'', in ji Likitan.

Nonon uwa

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Nonon uwa na da matuƙar muhimmanci wajen kare yaro daga kamuwa da cutuka

Babban abin da ke kare yara daga kamuwa daga cutar tamowa shi ne samun wadatacce kuma lafiyayyen nonon uwa.

Likitoci sun ƙarfafa gwiwar cewa ana buƙatar yaro ya samu aƙalla wata shida yana shan nonon uwa zalla kafin a fara ba shi wani nau'in abinci.

Saboda nonon uwa na ɗauke da tarin sinadaran da za su iya kare yara daga cututtuka kamar amai da gudawa da sauran cutuka masu alaƙa da yunwa.

Likitan ya ce iyaye ne ya kamata su kula da jariransu ta hanyar ba su nono ta hanyar cin abinci mai gina jiki kamar ganyayyaki da cin aƙalla ƙwai guda a rana, da kifi guda ɗaya a mako saboda su samu isasshen abinci da zai gyara musu ƙwaƙwalwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawarar cewa a riƙa bai wa jariri ruwan nono zalla na tsawon shekara biyu ko fiye.

Abinci mai gina jiki

..

Asalin hoton, Getty Images

Da zarar yaro ya fara cin abinci, abin da ya kamata a riƙa ba shi, shi ne nau'ikan abinci masu gina jiki, waɗanda su ne za su gina masa garkuwar jikinsa.

Masana sun ce ya kamata uwa ta mayar da hankali kan irin abinci mai gina jiki da ƴaƴanta za su ci.

Sun ce ya kamata uwa ta raba abincin zuwa guda biyu sannan ta zaɓi wanda ya dace da za ta bai wa yaronta.

Nau'ikan abincin da ke cikin wannan rukuni sun haɗa da kifi da wake da waken suya da ƙwai da madara da nama mai laushi da yaro zai iya haɗiya ba tare da ya zame masa matsala ba.

Ganyayyaki da ‘ya’yan itace

Asalin hoton, Getty Images

Kayan marmari
Bayanan hoto, 'Yayan itatuwa na taimaka wa ƙwaƙwalwar yaro wajen saurin fahimtar abubuwa

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce ya kamata kashi 50 na abincin da yara ke ci ya kasance ganyayyaki da kuma ‘ya’yan itatuwa.

Ganyayyaki na ɗauke da sinadaran 'vitamins' da 'mineral' da 'iron' da sauransu.

Sinadarin 'iron' na da matuƙar amfani ga ƙwaƙwalwar yaro a lokacin da yake girma, kamar yadda likitan ya yi bayani.

''Rashin abinci mai ɗauke da sinadaran mineral da 'vitamins' kan sa yaro ya samu rauni a ƙwaƙwalwarsa ta yadda zai kasa yin tunani mai amfani da zai amfanar wa al'umma''.

Ya ƙara da cewa bai wa yaro abinci mai ɗauke da waɗannan sinadaran zai taimaka masa wajen koyon karatu ko kuma aiki cikin kuzari.

''Sinadarin Folic na da muhimmanci ga rayuwar yaro, inda rashin sa zai janyo wasu abubuwa ga jariri''.

Mai ƙara kuzari

Dakta Auwal ya ce ana bukatar abinci mai ƙara kuzari, wanda yawanci dangin hatsi ke ɗauke da shi ya kai wani adadi a jikin yaro.

Nau'ikan abincin da ke cikin wannan rukuni sun haɗa da masara da shinkafa da taliya da alkama da biredi da doya da kuma rogo da dawa da gero da maiwa da sauransu.

Wannan nau'in abincin na samar da sinadaran ƙara kuzari da ke taimaka wa girman yaro.

Samun duka nau'in abinci a akushi guda

..

Asalin hoton, Getty Images

Likitan ya ce abin da ake buƙata shi ne a duk lokacin da za a bai wa yaro abinci to a lura cewa akwai aƙalla rukuni uku na azuzuwan abinci a cikin kwanon cin abinsa.

''Idan shinkafa zai ci ana so a samu wake, wanda ke cikin nau'in abinci mai gina jiki da ganyen salat wanda ke samar da sinadarin mineral element da mai wanda zai samar da sinarin daidaita zafin jiki, sannan a samu tumatir wanda ke samar da sinadarin vitamins'', in ji ƙwararren likitan abincin.

Yawar da kan iyaye

Dakta Auwal ya ce akwai buƙatar gwamnati ta riƙa wayar da kan mutane musamman domin su san irin yadda za su riƙa kula da yaransu, wajen ciyar da su abinci.

''Ya kamata gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu su riƙa shirya gangami ta tarurruka domin wayar wa iyaye kan kan irin abincin da ya kamata su bai wa yaransu don kauce wa kamuwa da cutar tamowa''.

''Saboda a wasu lokuta za ka ga mutum a ƙauye kaza ko zabuwarsa ta yi ƙwai, amma sai ya kwashe ya kai kasuwa ya sayar kuma ya sayo taliya, ko Bafulatana ta sayar da kindirmo wanda ke ɗauke da sinaran gina jiki, da na maiko, kuma ka ga ta sayo taliya wanda shi kuma ke dauke da sinadarin ƙara kuzari'', in ji ƙwararren likitan.

Ya ci gaba da cewa idan iyaye sun san abin da ke ƙunshe cikin ƙwai da kindirmon da kike sayarwa da ba su sayar suka sayi taliya ba'', in ji shi.

Haka kuma ya ce galibi a ƙauyuka inda matsalar ta fi ƙamari za ka tara da ire-iren abincin da ke da matukar amfani masu sauƙin samu, amma kuma rashin sani ya sa iyayen ba sa amfana da shi.

''Ire-iren abincin sun haɗa da zogale da ƙwayayen zaɓi da kaji da ganyen alayyaho da sauransu, waɗanda dukansa masu matuƙar amfani ne, amma rashin sani ya sa ba a amfana da arzikinsu'', in ji shi.

People are also reading