Ganduje: Abba Kabir Ya Shiga Matsala Bayan APC Ta Bankaɗo Makircin da Ya Ke Ƙullawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jam'iyyar APC ta bankaɗo makircin da aka hada game da zanga-zangar da aka gudanar a sakatariyarta.
A jiya Alhamis ne 25 ga watan Afrilu wasu 'yan jam'iyyar APC suka barke da zanga-zangar neman Abdullahi Ganduje ya yi murabus.
A cikin wata sanarwa da hadimin shugaban jam'iyyar APC, Kwamred Okpokwu Ogenyi ya zargi Gwamna Abba Kabir da hannu a zanga-zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ogenyi ya zargi sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature da daukar nauyin biyan masu zanga-zangar, cewar Daily Trust.
Ya ce an yi wa mutanen alkawarin N50,000 kowannensu inda daga bisani aka ba su N10,000 kacal, cewar rahoton Pulse.
Kamar yadda APC ta yi zargi, Bature ya tabbatarwa Gwamna Abba cewa yana da hukumomin tumbuke Ganduje daga kujerarsa.
Har ila yau, Ogenyi ya ce wasu daga cikin masu zanga-zangar 'yan Kwankwasiyya ne wanda suka manta suka sanya jajayen kaya.
Ya ce masu zanga-zangar sun tona asirin Bature ne bayan rashin cika musu alkawari wanda hakan ya fusata su.
"Mun samu bayanai cewa Gwamna Abba Kabir ya haɗa kai da wasu a Arewa ta Tsakiya tare da ware makudan kudade domin ganin ya kifar da Ganduje daga mukaminsa."
- Okpokwu Ogenyi
Kun ji cewa wasu matasa sun mamaye sakatariyar jam'iyyar APC inda suka bukaci shugabanta, Abdullahi Ganduje ya yi murabus.
Mutanen wadanda suka bayyana kansu a matsayin mambobin jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya sun nuna damuwa kan shugabancin tsohon gwamna.
Asali: Legit.ng