Home Back

Lokaci Ya Yi: Kwamishinan Bauchi Ya Rasu Yana da Shekara 60 a Duniya

legit.ng 2024/7/3

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Bauchi, Ahmed Jalam ya rasu.

Marigayin ya rasu ne tare da direbansa a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Misau zuwa Darazo a jihar Bauchi a ranar Asabar, 1 ga watan Yunin 2024.

Ahmed Jalam ya rasu
Ahmed Jalam ya rasu yana da shekara 60 Hoto: Ahmed Jalam Asali: Facebook

An bayyana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa garin Jalam ne a ƙaramar hukumar Dambam a lokacin da hatsarin ya auku, cewar rahoton jaridar The Punch.

Gwamnan Bauchi ya yi ta'aziyya

Da yake miƙa saƙon ta'aziyyarsa, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar Ahmed Jalam a matsayin wani babban rashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana cewa rasuwarsa ta bar giɓi saboda jajircewarsa wajen yiwa al'umma hidima.

“Mutuwar kwamishinan ta bar babban giɓi a jihar kuma ta jefa mutanen jihar cikin alhini saboda yadda ya yi suna wajen sadaukar da kai da jajircewarsa wajen yin hidima."
"Ahmad Jalam ya riƙe muƙamin kwamishinan harkokin addini a shekarar 2019 kuma an sake naɗa shi matsayin kwamishina a shekarar 2023 kuma ya yi aiki a ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu har zuwa ƙarshen rasuwarsa."

- Sanata Bala Mohammed

Kwamishinan ya rasu yana da shekaru 60 a duniya kuma ya bar mata da ƴaƴa.

Za a yi sallar jana’izarsa a safiyar ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinsu na Jalam.

Asali: Legit.ng

People are also reading