Home Back

Dalilin da ya sa na maida naira miliyan 1.6 dana tsinta a Makka – Alhajin Jigawa

premiumtimesng.com 2024/7/3
Dalilin da ya sa na maida naira miliyan 1.6 dana tsinta a Makka – Alhajin Jigawa

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta yabawa wani Alhajin jihar Jigawa daya tsinci wasu makudan dalolin kasar Amurka, Rasha da kuma Riyal na kasar Saudi Arebia masu yawa a Masallaci mai tsarki na Harami kuma yaji tsoron Allah ya dawo da kudaden domin a baiwa mai su.

Alhajin na Jigawa mai suna Alhaji Abba Sa’adu Limawa daya fito daga karamar hukumar Dutse, wanda kuma daraktan kula da harkokin kasuwanci ne a wani gidan Rediyo a Dutse, wanda hukumar NAHCON ta yaba masa tare da kiransa da sunan Alhaji daya nuna tsoron Allah a cikin Alhazan Najeriya a wannan shekara.

Yawan kudaden da Alhajin na Jigawa ya tsinta a masallacin na Harami sun kai Dala dari takwas da kuma Riyal dari shida da casa’in, sai takardun kudaden kasar Rasha da yawansu ya kai Rouble dubu goma da dari biyar.

Da yake zantawa da manema labarai a Makka Muhammad Alhaji Abba Sa’adu ya bayyana yadda ya tsinci makudaden kudaden a cikin masallacin Harami, da kuma yadda yaji tsoron Allah yaje ya nemi shugaban hukumar kula da jin dadi Alhazai ta jihar Jigawa domin a nemi wanda ya manta kudaden nasa.

Yanzu haka dai wannan Alhaji na jihar Jigawa Alhaji Abba Sa’adu Limawa daya nuna wannan hali na gari da tsoron Allah na cigaba da samun yabo daga manyan mutane, kuma hukumar NAHCON a karkashin shugaban ta Malam Jalal Ahmad Arabi yasha alwashin kai makuden ga hukumomin kasar Saudi Arebia domin a baiwa mai su.

People are also reading