Home Back

Gwamnan Zamfara na Shan Sukar Gina Filin Jirgin Saman N62.8b Ana Fama da ’Yan Bindiga

legit.ng 2024/7/2
  • Gwamantin jihar Zamfara karkashin Dauda Lawal na cigaba da shan kakkausan suka kan kudurin gina filin jirgin sama a jihar
  • Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya caccaki gwamnatin bisa kudurin tare da bayyana abin da ya kamata Dauda Lawal ya yi a wannan lokacin
  • Gwamna Lawal ya dauki aniyar kashe kudi kimanin Naira biliyan 62.8 domin gina katafaren filin jirgin sama a babban birnin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Ana cigaba da sukan gwamna Dauda Lawal bisa aniyar gina katafaren filin jirgin sama a jihar.

Gwamna Dauda Lawal zai kashe kudi kimanin Naira biliyan 62.8 domin gina filin jirgin sama a Gusau.

Jihar Zamfara
An soki gwamna Dauda Lawal kan gina filin jirgin sama a Zamfara. Hoto: Dauda Lawal Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito shahararren dan siyasa a jihar, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi na cewa aikin bai dace ba a wannan lokacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A maida hankali kan tsaro a Zamfara

Tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara karkashin jam'iyyar AFGA, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya ce ba buƙatar filin jirgin sama a jihar Zamfara yanzu.

Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya ce abin da mutane ke buƙata shi ne maganin yan bindiga da samar da abubuwan more rayuwa.

Shinkafi: "Filin jirgin N62.8b ya yi tsada'

Har ila yau, Dakta Shinkafi ya ce ko da za a gina filin jirgin saman bai kamata a ce an ware kudi har N62.8b ba a cewar rahoton Vanguard.

Shinkafi ya ce gwamna Dauda Lawal ya ruɗi ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo kan cigaba da aikin duk da cewa ba shi ya kamata a kashewa kudin ba.

Zamfara: Filin jirgin sama ya gagara ginuwa

Aikin filin jirgin saman birnin Gusau dai ya samo asali ne tun a lokacin mulkin gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi.

Haka aka cigaba da tafiya karkashin gwamnonin da suka gabata ba tare da an yi aikin ba har wannan lokaci.

Jirgi ya 'jefa' bam a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa mazauna ƙauyen Kukawa a karamar hukumar Maradun a Zamfara sun yi ikirarin sojoji sun masu ruwan bama-bamai a filin idi.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jirgin ya zo wucewa sai ƴan bindiga suka buɗe masa wuta bisa haka ya saki bam ɗin da ya shafi fararen hula.

Asali: Legit.ng

People are also reading