Home Back

Kano: Tashin Hankali Yayin da Sarki Sanusi II da Aminu Ado Ke Shirin Sallar Jumu'a a Wuri Ɗaya

legit.ng 2024/7/6

Kano - Mutanen sun fara fargaba da ɗar-ɗar yayin da ake sa ran mai martaba Sarkin Kano da aka mayar, Muhammadu Sanusi II zai jagoranci sallar Jumu'a a masallacin fada.

Ana tsammanin Sanusi II zai yi limancin sallah raka'a biyu ta Jumu'a a babban masallacin Jumu'a na fadar sarki yau 31 ga watan Mayu, 2024.

Damburan Kano ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu da yammacin ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sanarwar da Danburan Kano ya fitar ta gayyaci ɗaukacin al'ummar jihar su zo su saurari huɗubar Jumu'a da Sanusi III zai gabatar a masallacin fadar sarki.

Sai dai abin da ya sa mutane suka fara fargaba shi ne, Ssrkin Kano na 15 da aka tsige, Aminu Ado Bayero, ya shirya yin sallar Jumu'a a masallacin fada.

A wata sanarwa da hadimin Aminu Ado ya fitar, ya gayyaci jama'a su biyo basarakwn zuwa masallacin fada domin yin sallar Jumu'a yau.

Ya ƙara da cewa Aminu Adi Bayero zai fito ya kama hanyar zuwa babban masallacin Jumu'a na fada da misalin ƙarfe 12:30.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har kawo yanzu hukumar ‘yan sanda ba ta ce uffan ba game da wannan lamari ɗa ke shirin faruwa wanda ka iya haɗa sarakunan biyu a wuri ɗaya.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna ya ci tura saboda lambar wayarsa ba ta shiga ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading