Home Back

Louisiana ta amince da hukuncin dandatsa ga masu fyade

dw.com 2024/7/3
Hoto: (Hilary Scheinuk/AP Photo/picture alliance

Louisiana ta zamo jiha ta farko a Amurka da ta amince da hukuncin dandantsa kan duk namijin da aka kama da laifin cin zarafin kananan yara, da ya hada da fyade da muzgunawa.

Gwamnan jihar Jeff Landy ne ya sanya hannu kan dokar, wadda za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, da za ta bai wa alkalai damar yankewa duk wanda aka samu da laifin lalata kananan yara 'yan kasa da shekaru 13 hukuncin fidiye shi.

Yanzu haka dai akwai mutane 2,224 daure a kurkukun jihar ta Louisiana da ke fuskantar tuhuma, kan laifin yi wa kananan yara fyade, ko da yake sabuwar dokar ba za ta yi aiki a kansu ba, kasancewar ana zarginsu ne kafin kafa dokar.

People are also reading