Home Back

Kuri’ar CGTN: 90.1% Na Masu Bayyana Ra’ayi Na Kallon Amurka A Matsayin Maras Ikon Tankwara Doka

leadership.ng 2024/6/29
Kuri’ar CGTN: 90.1% Na Masu Bayyana Ra’ayi Na Kallon Amurka A Matsayin Maras Ikon Tankwara Doka

Kasar Amurka ta sake amfani da takunkumai wajen hawa kujerar naki, game da takardar sammacen cafke firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da wasu karin mutanen da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta fitar.

Wannan dai mataki ya sanya al’ummun kasa da kasa sukar lamirin Amurka. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta kaddamar ta nuna cewa, kaso 90.1 bisa dari na wadanda suka bayyana matsayar su na kallon Amurka a matsayin wadda ba ta da ikon tankwara doka, sun kuma soke ta bisa yadda take kin martaba matsayar hukumomin kasa da kasa, da watsi da doka.

Ba dai wannan ne karon farko da Amurka ta yi yunkurin kakabawa kotun ta ICC takunkumi ba. A shekarar 2020 ma, shugaban Amurka na wancan lokacin Donald Trump, ya fitar da dokar shugaba, wadda ta ce Amurka za ta kakabawa jami’an kotun ICC takunkumai, sakamakon yunkurin binciken Amurka, don gane da yadda ta gudanar da yaki a Afghanistan. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

People are also reading