Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Darasi Daga Zanga-zangar Kenya: Idan Gemun Ɗan’uwan Ka Ya Kama Wuta, Shafa Wa Naka Ruwa

premiumtimesng.com 2024/8/22
RA’AYIN PREMIUM TIMES: Darasi Daga Zanga-zangar Kenya: Idan Gemun Ɗan’uwan Ka Ya Kama Wuta, Shafa Wa Naka Ruwa

Ya kamata a ce tun farko Najeriya ta koyi darasi daga zanga-zangar fushin ƙarin kuɗin haraji, wadda ta ɓarke a ƙasar har ya yi wa tattalin arzikin Kenya mummunar illa.

Zanga-zangar Kenya ta ɓarke ne yayin da Shugaban Kenya William Ruto ya bijiro da wasu tsare-tsaren ƙara ɗirka wa ‘yan ƙasar haraji, domin samun ƙarin kuɗaɗen shiga. Kuma amincewar da ‘yan majalisar Kenya suka yi da dokar ƙarin harajin ce ta tunzura jama’a har suka ɗauki doka a hannun su, aka yi mummunan tashin hankali na tsawon kwanaki.

Tilas aka haƙura aka janye ƙudirin neman kafa dokar, saboda an ga tashin hankali na neman durƙusar da ƙasar kuma ya kifar da gwamnatin ta Ruto.

Asalin rikicin Kenya dai gwamnatin ce ta damu da ɗimbin bashin Dala biliyan 80 da ake bin ta, wanda fiye da rabin kuɗin shigar da gwamnatin ƙasar ke samu duk wata, ya na tafiya ne wajen biyan bashi. Ganin haka sai ta nemi ƙara Harajin Jiki Magayi kan ‘yan ƙasar.

Su kuma talakawa suka ga ƙarin kashi 16 bisa 100 na Harajin Jiki Magayi (VAT) ya ƙara farashin biredi da sukari, man girki da duk wani kayan da ake shigowa ko ake sarrafawa a Kenya, ciki hara da audugar ƙunzugu da mata ke amfani da ita a lokacin jinin al’ada, sai aka fara nuna rashin amincewa.

Matasa waɗanda suka shiga sahun-gaban zanga-zangar Kenya marasa aikin yi ne, waɗanda yunwa ta ci ta rarake masu ciki, babu komai a cikin su sai haushi da ƙufula da ɗacin ran raɗaɗin tsadar rayuwa. Sai suka yi wa wannan ƙarin kuɗin Harajin Jiki Magayi (VAT) kallon tamkar wata makara ce gwamnati ta kinkimo domin ya riƙa jidar su ta na kaiwa maƙabarta a daidai lokacin da su ke shure-shuren mutuwa saboda yunwa, maimakon ta ba su abinci su ci har su farfaɗo.

Tarzoma fa ta ɓarke, kuma ta yi muni. Sojoji da ‘yan sanda suka kashe na kashewa, amma duk aka kasa shawo kan lamarin. A ƙarshe tilas Ruto ya janye. To wannan hannun ka mai sanda ne ga dukkan mai hankali. A mulkin dimokraɗiyya ba a yin wasa da ra’ayin mafiya yawan ɗaukacin jama’ar ƙasa.

Darussan da Najeriya ya kamata ta koya daga zanga-zangar Kenya su na da yawa, ga su kan su hukumomin gwamnati da kuma matasa. Saboda akwai kamanceceniya tsakanin matsalar da Kenya ta fuskanta da kuma ta Najeriya. A Legas da sauran manyan garuruwan ƙasar nan, mutane na ta nuna hasala da ƙufula saboda halin raɗaɗin yunwa da ake fama a cikin ƙasa. A kullum farashin kayan abinci da kayan masarufi sai ƙara tashi suke yi. Ga kuma yadda rashin aikin yi ke ci gaba da ƙaruwa. Tuni ma an fara ‘yar zanga-zanga nan da can a wasu wurare, amma dai ta lumana.

Amma fa akwai matuƙar tsoron cewa kakabi da hayagagar da ake kan yi za ta iya zarcewa inda ba a buƙata ko fatan a kai ƙasar nan ga afkawa.

Kada a manta, zanga-zangar #EndSARS a cikin 2020 ai ba ta magance irin cin zalin ɗin da ‘yan sanda ke yi wa jama’a ba. Saboda har yanzu ba su daina ba. Jami’an SARS da aka rushe, an maida su cikin game-garin ‘yan sanda sun ci gaba da gallaza wa jama’a.

Maimakon matasa su haifar da tarzoma, kamata ya yi su tashi tsaye su shiga cikin siyasa dumu-dumu, su shiga jam’iyyu inda a ciki za su samu nasarar samun damar neman kawo nagartaccen tsarin dimokraɗiyya.

Shi kuwa Shugaba Bola Tinubu, kada ya bari ya faɗa ko ya jefa kan sa cikin irin tarkon da ya kama Ruto na Kenya. Ya gaggauta buɗe ƙofofin tattaunawa. Kada ya toshe kunnen sa daga jin muryoyin masu adawa da shi. Ya saurari ra’ayin su.

Sauye-sauyen da Tinubu ya bijiro da su tun daga kan cire tallafin fetur da sauran tsauraran matakan da suka haifar da raɗaɗi da masifar tsadar rayuwa, duk su na nuna cewa tamkar wata nakiya ce ya riƙa binnewa a kan hanya.

Babbar matsalar da ake fuskanta a yanzu ita ce tsada da ƙarancin abinci. Kuma har yanzu fiye da shekara ɗaya kenan an kasa cimma matsaya kan batun mafi ƙanƙantar albashi, bayan harankazamar tsarin tallalin arzikin da Tinubu ya ɓullo da shi ya karyar da darajar Naira.

Bashin da ake bin Najeriya sai ƙaruwa ya ke yi. Zuwa Disambar 2023 ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 97. Amma zuwa watan Maris 2024 har bashin ya kai Naira Tiriliyan 121.67, wato Dala biliyan 92.46.

Cikin makon da ya kamata kuma NNPC ta shiga duniya neman bashin Dala biliyan 2, wanda ta ce za a riƙa biya da ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa. Kuma a daidai lokacin kamfanin ke neman Dala biliyan 3.3 daga Afreximbank. Wannan zai ƙara malejin bashin ya kai Dala biliyan 93.46 kenan. Wannan kuwa ba labari ba ne mai daɗin ji da gani ko kaɗan.

Wannan gwamnatin za ta yi wa kan ta ‘ƙiyamul laili’ idan ta rage kashe kuɗaɗen gwamnati barkatai, kuma ta toshe hanyoyin da kuɗaɗen gwamnati ke zurarewa, ta ƙwato kuɗaɗen da ɓarayin gwamnati suka sace ba tare da tsoron wane ko wani ba.

Idan jama’a suka ga gwamnati na yin haka, to za su ba ta amannar cewa da gaske ta na iya bakin ƙoƙarin ta wajen fitar da su daga masifun da ke addabar su, waɗanda kuma ita gwamnatin ce musabbabin jefa al’ummar ta cikin waɗannan masifun ƙunci, tsada da raɗaɗin tsadar rayuwa.

People are also reading