Home Back

'Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Shugaban Jami'a Ana Taron Zaman Lafiya

legit.ng 2024/7/7
  • A cigaba da kai hare-hare da yan bindiga suke a Arewacin Najeriya sun kai hari tare da kashe wani babban malamin jami'a a hanyar Zamfara
  • Malamin jami'ar mai suna Farfesa Yusuf Saidu ya kasance daya daga cikin shugabannin jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto
  • Yan bindigar sun kai harin ne yayin da ake tsaka da yin taro na musamman a jihar Katsina domin shawo kan matsalolin tsaro a Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Yan bindiga sun kai hari mummuna a hanyar Zamfara yayin da ke tsaka da taro kan magance matsalolin tsaro a yankin Arewa maso yamma.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar Farfesa Yusuf Saidu na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke jihar Sokoto.

Farfesa Yusuf Saidu
Yan bindiga sun kashe malamin jami'a a Zamfara. Hoto: Usmanu Danfodiyo University Sokoto Asali: Facebook

Legit ta tabbatar da kisan Farfesa Yusuf ne a cikin wani sako da jami'ar Danfodiyo ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun kashe shugaba a jami'a

Bayanan da jami'ar Usman Danfodiyo ta wallafa sun yi nuni da cewa Farfesa Yusuf Saidu ya hadu da tsautsayin ne yayin da yake tafiya daga Sokoto zuwa Kaduna.

A lokacin da Farfesan ke tsaka da tafiyar ne a yankin Kucheri na Zamfara 'yan bindigar suka kai masa hari tare da nasarar hallaka shi nan take kuma sun jikkata direbansa.

Rahotanni sun nuna cewa Farfesan ya biyo hanyar ne jim kadan bayan an fafata tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga, sai suka yi zaton 'yan sanda ne suka dawo wurin sai kawai suka bude masa wuta.

Halin Farfesa Yusuf Saidu

Jami'ar Danfodiyo ta tabbatar da cewa Farfesa Yusuf Saidu ya kasance mutum ne mai hazaka da kwazo sosai.

Makarantar ta kuma yi kari da cewa Farfesan ya kasance mai riko da addinin da riko da gaskiya da amana.

Matsayin Farfesa Yusuf a jami'a

Legit ta gano cewa Farfesa Yusuf Saidu yana rike da matsayin mataimakin shugaban jami'a (DVC) a bangaren bincike.

Jami'ar Danfodiyo ta mika sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar, jami'ar, iyalasa da Najeriya baki daya.

'Yan bindiga sun kai hari Filato

A wani rahoton, kun ji cewa sama da mutane 40 ne 'yan bindiga suka kashe a mummunan harin da suka kai kauyen Zurak da ke jihar Plateau.

Mazauna yankin sun ce ba su iya kai rahoton faruwar lamarin ga jami'an tsaro ba saboda rashin kyawun hanyar sadarwa da suke fama da ita.

Asali: Legit.ng

People are also reading