Home Back

Matasa Za Su Amfana Da Shirin Noma Don Samun Riba

leadership.ng 2024/8/24
‘ATASP-1

Gwamnatin tarayya ta sanya matasa 200 cikin shirinta na bunkasa noma, wanda ake kira da ‘ATASP-1’.

Matasan da za su amfana da wannan shiri, an zabo su ne daga sassa daban-daban guda hudu na fadin kasar nan.

Jami’in shirin na kasa, mai kula da shiyoyin Jihohin Kano da Jigawa; Dakta Ibrahim Muhammed Arabi ne, ya sanar da hakan a lokacin bude taron shirin.

Arabi, wanda jami’in da ke kula da aikin noma; domin riba na kasa kan shirin, Dakta Kunle Alege ya wakilce shi a wajen taron; ya ce a karkashin shirin za a horas da matasa 50 wadanda aka zabo daga kowace shiyya guda ta kasar nan, wanda hakan ya sanya adadin matasan suka kai 200.

Ya kara da cewa, za a koyar da matasan yadda za su aiwatar da noman, don kasuwancin zamani tare kuma da yin amfani da dabarun zamani; domin cimma nasarar shirin.

A cewarsa, bayan an horar da matasan za kuma ci gaba da biyan su tare da tallafa masu da kudade; domin samun damar gudanar da aikin yadda ya kamata.

Shi ma wani jami’i, a sashen cibiyar aikin noma ta (IITA), Dakta Alpha Kamara ya bukaci matasan da su yi amfani da horon da aka ba su, don zama masu dogaro da kawunansu ta hanyar aikin noma.

People are also reading