Shugabannin APC Za Su Sanya Labule da Ganduje a Abuja, Bayanai Sun Fito
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Shugabannin mazaɓu na jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, za su ziyaci shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje a birnin tarayya Abuja.
Hakan na zuwa ne dai bayan wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar na mazaɓar Ganduje sun sanar da dakatar da tsohon gwamnan na jihar Kano, cewar rahoton jaridar The Punch.
Shugabannin za su ziyarci Ganduje ne a ranar Laraba, 17 ga watan Afirilun 2024 domin jaddada goyon bayansu a gare shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ziyarar wacce aka shirya, za ta gudana ne a sakatariyar jam'iyyar APC ta ƙasa da misalin ƙarfe 11:00 na safe, rahoton Naija News ya tabbatar.
Hakan na zuwa ne dai kwana biyu bayan mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a a mazaɓar Ganduje, Halliru Gwarzo, ya dakatar da Ganduje daga jam'iyyar.
Gwarzo, wanda ya yi magana da ƴan jarida a Kano, ya ce shugabannin jam'iyyar sun ɗauki matakin dakatarwar ne saboda zarge-zargen cin hanci da ake yi wa Ganduje.
Ya kafa hujja da tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa waɗanda gwamnatin jihar Kano ke yi wa tsohon gwamnan inda aka shirya gurfanar da shi a ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilun 2024.
Sai dai, shugabannin jam'iyyar APC a matakin jiha sun yi fatali da dakatarwar tare da dakatar da Gwarzo da sauran shugabannin jam'iyyar da ke da hannu a lamarin na tsawon watanni shida.
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani mai zafi kan dakatar da shugabanta na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Jam'iyyar ta shigar da ƙara a gaban babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, kan waɗanda suka kitsa dakatar da Ganduje.
Asali: Legit.ng