Home Back

EURO 2024: Magoya Bayan Jamus 378,000 Sun Shigar da Korafin Sake Buga Wasan Jamus da Sifaniya

premiumtimesng.com 2024/8/22
EURO 2024: Magoya Bayan Jamus 378,000 Sun Shigar da Korafin Sake Buga Wasan Jamus da Sifaniya

Aƙalla magoya bayan tawagar kwallon kafa ta ƙasar Jamus 378,000 ne suka rattaba hannu kan takardar neman a sake buga wasan kusa da na karshe na gasar EURO 2024 da ƙasar Sipaniya.

Sun shigar da karafin ne saboda irin rawar da Anthony Taylor ya taka a matsayin sa na alkalin wasa, wajen cire ƙasar Jamus daga gasar

An gano cewa magoya bayan sun zargin Taylor da hana Jamus bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan kwallo ta taɓa hannun Marc Cucurellla a yadi na 18.

Wanda suka kirkiri damar shigar da korafin change.org sun jaddada cewa a shirye suke su fuskanci kowacce iri barazana daga hukumar kwallon kafa ta Nahiyyar Turai UEFA.

Sifaniya ta yi nasarar tsallakawa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024 bayan doke masu masaukin baƙi Jamus 2-1.

Wannan na ɗaya daga cikin wasannin da ake hanƙoron gani a gasar ganin yadda tawagogin biyu suka zama mafiya hazaƙa, kuma wasan bai ba wa ‘yan kallo kunya ba.

Dani Olmo ne ya fara ci wa Sifaniya ƙwallo a minti na 51, inda har sai da ta kai saura minti biyu lokaci ya cika sannan F. Wirtz ya farke wa Jamus.

Kazalika, ‘yan ɗaƙiƙoƙi ne suka rage a shiga bugun finareti bayan cikar zagayen ƙarin lokaci Mikel Merino ya lallaɓo ya cinye Jamus da ka bayan Olmo ya bugo ƙwallo a sama.

People are also reading