Home Back

Ana ce-ce-ku-ce kan zargin tsohon shugaban Nijar Issoufou da danne kuɗin sayen jirgin sama

bbc.com 2 days ago

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Muhammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar cacar baki ta barke bayan sanarwar kamfanin Orano, mai hakar ma'adanai dake cewa shi ya sayi jirgin shugaban kasar Nijar a shekarar 2014.

Hakan dai ya biyo bayan kwace lasisin hakar ma'adanin Uranium a daya daga cikin manyan cibiyoyi da ke arewacin kasar, daga hannun kamfanin.

Sai dai a baya lokacin da ake kiran kamfanin Orano da sunan Areva, da kansa ya musanta batun da ke cewa ya bai wa gwamnatin Nijar din kudin sayen jirgin.

A shekarar 2015 ne gwamnatin Shugaba Muhammadou Issoufou ta sayi sabon jirgin shugaban kasa, tun daga lokacin takaddama ta barke kan hakan.

Batun ya janyo muhawara tsakanin wakilan majalisun Nijar, babban abin da ya janyo hakan kuwa yana da nasaba da batun masumagana da yawun masu rinjaye ya yi cewa za a sayi jirgin ne da kudin da aka samu daga kamfanin hakar ma'adinai na Areva wanda a yanzu aka sauya masa suna zuwa Orano.

To amma cikin gaggawa kamfanin Areva na kasar Faransa da bangaren gwamnatin Issoufou sun musanta hakan.

Shekara goma da yin wannan, bayan sojojin Nijar sun hambarar da mulkin Shugaba Muhammad Bazoum da ya gaji mulkin daga Muhammadou Issoufou, gwamnatin mulkin sojan suka sanar da karbe lasisin hakar ma'adinin Uranium daga Orano.

Shi ne kamfanin ya yi amai ya lashe tare da tabbatar da cewa da kudinsa aka sayi jirgin na shugaban kasa a zamanin mulkin Muhammadou Issoufou.

Tuni wasu yan kasar suka fara nuna yatsa ga tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou suna zarginshi da yin rubda ciki da kudin sayen jirgin.

Amma wani na hannun daman tsohon shugaban mai suna Ousmanou Muhammadou ya ce lamarin ba haka yake ba: ''Idan cin hanci aka ba da to kasar Nijar aka bai wa, jirgi da aka saya dai na shugaban kasar Nijar ne, kuma yana hannun gwamnatin mulkin soji.

Wadanda suke wadannan zantuka ba su da aikin yi, daman sun jima suna son a kama Muhammadou Issoufou, kuma ba ya tsoron a yi bincike domin gano gaskiyar lamarin,'' in ji Ousmanou.

Tuni kungiyoyin farar hula a jamhuriyar Nijar suka fara tsokaci kan wannan, daya daga cikinsu shi ne Bane Ibrahim da ya ce bincike ne kadai zai sanya a gano gaskiyar lamarin, ana bukatar bincikar gwamnatin Muhammadou Issoufou da kamfanin Orano.

Ya kara da cewa: ''Akwai matsala, tun da gashi mun gano kamfanin Arano wato Areva a baya shi ya sai jirgi ya bai wa Nijar, ya kamata a lalubo gaskiya tun da a baya sun musanta hakan. Saboda indai Orano ne ya sayi jirgin, to an handame kudin Nijar, ya kamata a yi bayanin inda kudin suka shiga, saboda maganar da ake yi kudaden sun kai Miliyar 21 na CFA'.

A yanzu dai kallo zai koma sama na ganin ko hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar za su dauki matakin bincikar tsohon shugaban kasa Muhammadou Issoufou kan wannan danbarwa, wanda daman tun a baya suke ta kiraye-kirayen a gurfanar da shi kan zargin badakalolin rashawa da dama.

People are also reading