Home Back

El-Rufai Ya Maka Majalisar Kaduna A Kotu Kan Zargin Karkatar Da Biliyan 432

leadership.ng 6 days ago
Kwamitin Majalisar Kaduna Ya Bayar Da Shawarar A Binciki El-Rufai

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai karar majalisar dokokin jihar kan zargin gwamnatisa da karkatar da Naira biliyan 432.  

Majalisar ta yi zargin cewa ya yi amfani da Naira biliyan 432 ba bisa ka’ida ba a tsawon wa’adinsa na shekaru takwas, wanda ya hakan ya jefa jihar cikin kangin bashi.

Lauyan El-Rufai, Abdulhakeem Mustapha, ya shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Laraba.

Lauyan ya kalubalanci rahoton majalisar da ya zargi El-Rufai da karkatar da dukiyar jama’ar jihar.

Kwamitin majalisar dokokin jihar, ya yi bincike game da wasu kudade, bashi da kwangiloli da El-Rufai ya bayar a lokacin mulkinsa.

Kakakin El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya ce har yanzu ba su samu rahoton ba amma za su yi martani da zarar sun samu rahoton.

Ya jaddada cewar gwamnatin El-Rufai, ta yi aiki bisa gaskiya, inda ya ce sun yi watsi da ikirarin majalisar dokokin.

People are also reading