Home Back

Turkiyya ta tsare mutane 8 da ake zargi da yi wa Isra’ila leken asiri

premiumtimesng.com 2024/5/6
Turkiyya ta tsare mutane 8 da ake zargi da yi wa Isra’ila leken asiri

‘Yan sandan Turkiyya sun tsare wasu mutane takwas da ake zargi da sayar da bayanai ga hukumar leken asirin Isra’ila, Mossad, in ji ministan cikin gidan kasar Ali Yerlikaya a yau Juma’a.

Ya ce wadanda ake zargin sun yi taro da jami’an leken asirin Isra’ila tare da tattara bayanai kan daidaikun mutane da kamfanoni a Turkiye da Mossad ke fako.

Ya kara da cewa an yi zargin sun mika bayanan da takardu ga jami’an leken asirin Isra’ila.

An gudanar da samamen tare da hukumar leken asiri ta kasar Turkiyya a cewar ministan.

People are also reading