Home Back

Majalisar Ministocin Iran Ta Shiga Taron Gaggawa Bayan Mutuwar Shugaban Ƙasar

leadership.ng 2024/6/16
Majalisar Ministocin Iran Ta Shiga Taron Gaggawa Bayan Mutuwar Shugaban Ƙasar

Majalisar Ministocin ƙasar Iran ta kira wani taron gaggawa na biyu cikin ƙasa da sa’o’i 24 bayan tabbatar da mutuwar shugaba Ebrahim Raisi.

Kafofin yaɗa labarai na cikin gidan ƙasar sun ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban ƙasar Iran Mohammad Mokhber ne ya jagoranci wani taro a yammacin Lahadi bayan da wani jirgi mai saukar ungulu ya bace tare da mutane tara a cikinsa a yankin Arewa maso Yammacin Iran.

Rahoton ya bayyana cewa Ministan harkokin wajen ƙasar Hossein Amirabdollahian shi ma ya rasu a haɗarin jirgin saman.

Raisi da Amirabdollahian dai suna hanyarsu ne ta dawowa daga wata ganawa da shugaban ƙasar Azarbaijan Ilham Aliyev ne lokacin da jirgin nasu ya ɓace na’urar hange ta (Radar) a yammacin Lahadi.

Bisa ga tsarin mulkin ƙasar, bayan mutuwar Raisi, Mokhber zai ci gaba da mulki, tare da jiran amincewa daga Jagoran Koli Ayatullah Ali Khamenei, daga nan kuma sai a gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 50.

Tuni dai ƙungiyar Hamas ta aike da saƙon gaisuwa ga gwamnati da mutanen ƙasar Iran, inda ta bayyana cewa lallai wannan babban rashi ne gare su. Hamas na daga cikin ƙungiyoyin da suke samun tallafi daga ƙasar Iran sosai a yaƙin da suke yi da Yahudawa ƴan kama wuri zauna.

People are also reading