Home Back

Ba Zan Taba Mantawa Da Liverpool A Rayuwata Ba – Jurgen Klopp

leadership.ng 2024/6/26
Ba Zan Taba Mantawa Da Liverpool A Rayuwata Ba – Jurgen Klopp

A ranar Lahadi kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya jagoranci wasansa na ƙarshe a matsayin kocin ƙungiyar bayan shafe shekaru 9 a Anfield.

Klopp wanda tsohon kocin Borrusia Dortmund ne ya lashe kofuna 8 a Liverpool da suka haɗa da; Gasar Zakarun Turai da Firimiya da UEFA Super Cup a shekarun da ya kwashe a ƙungiyar.

Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Jurgen Klopp
Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Jurgen Klopp

A wasansa na ƙarshe a ranar Lahadi Liverpool ta doke ƙungiyar Wolverhampton Wanderers da ci 2-0 a filin wasa na Anfield.

Bayan an tashi daga wasan magoya bayan Liverpool sun yiwa kocin nasu bankwana mai ƙayatarwa yayinda ya tabbatar da cewar ba zai taba mantawa da ƙungiyar a rayuwarsa ba.

People are also reading