Home Back

Shugaban kasar Tunisiya ya kori ministan harkokin addini bayan mutuwar Alhazai 49 A Aikin Hajji

premiumtimesng.com 2024/7/1
Hajji Kaaba
Hajji Kaaba

Shugaban kasar Tunusiya Kais Saied, ya kori ministan harkokin addini a kasar bayan da ‘yan Tunisiya 49 suka mutu a aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.

Adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 1126, fiye da rabinsu daga Masar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar a ranar Juma’a, inda suka hada bayanai a hukumance da kuma rahotanni daga jami’an diflomasiyya da ke da hannu.

A ranar Talata ma’aikatar harkokin wajen Tunisia ta ba da rahoton mutuwar mahajjata 35 ‘yan kasar Tunusiya, amma adadin ya karu zuwa 49 a cewar kafafen yada labarai na Tunisiya.

Ma’aikatar ba ta fayyace ko mutuwar na da nasaba da yanayin zafi ba, ta kara da cewa galibin wadanda suka mutu sun tafi Saudiyya ne da bizar yawon bude ido ne.

Haka kuma rahotanni daga kasar Amurka, wata ta rasa iyayenta biyu a Saudiyya yayin aikin Hajji.

A Najeriya, an samu waɗanda suka rasu da dama lokacin aikin Hajji na bana.

People are also reading