Home Back

Tinubu Ya Dauki Zafi Kan Ministocinsa, Ya Fadi Wadanda Zai Kora Daga Mukamansu

legit.ng 2024/6/26
  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tabbatar da aniyarsa ta korar ministocin da suka gaza yin katabus a gwamnatinsa
  • Tinubu ya godewa duka ministocinsa saboda kokarin da suke yi sai dai ya ce zai sallami duk wanda ya gaza yin wani abin kirki ga ƴan Najeriya
  • Shugaban ya bayyana haka ne a yau Alhamis 30 ga watan Mayu yayin taro da shugabannin Arewa Consultative Forum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai kori duka ministocinsa da ba su tabuka komai ba.

Shugaban ya bayyana cewa zai ci gaba da kawo ababan more rayuwa ga al'ummar Najeriya baki daya.

Tinubu ya tabbatar da zai kori wasu daga cikin ministocinsa
Bola Tinubu ya sha alwashin korar wasu daga cikin ministocinsa da suka gaza. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu. Asali: Twitter

Tinubu ya godewa ministocinsa kan kokarinsu

Tinubu ya fadi haka ne yayin hira da shugabannin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) a fadarsa da ke Abuja, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ya godewa duka ministocinsa da masu mukamai sai dai ya ce duk wanda ya gaza zai raba shi da kujerarsa.

"Ina godewa duka ministocina da irin kokarin da suke yi, sai dai kuma duk lokacin dana fahimci sun gaza wurin bautar ƴan Najeriya zan kore su."
"Ina rokon ku da ku kira gwamnoni, ina iya bakin kokarina wurin tabbatar da samar da kudi ga Najeriya."
"Dole su ma su tausaya wurin duba zuwa ga mutane da ke karkashinsu a wannan lokacin."

- Bola Tinubu

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading