Home Back

Musulmai Sun Yabawa Dangote Bayan Ba da Tallafi Ga Ƙananan Hukumomi 16 a Jiha 1

legit.ng 2024/5/18
  • Al'ummar Musulmai sun yabawa attajirin Nahiyar Afirka, Aliko Dangote kan irin gudunmawar da ya basu a jihar Ekiti
  • Shugabannin Musulmai a jihar sun gode masa kan ba da tallafin wanda ya zaga dukkan ƙananan hukumomi 16 a jihar
  • Shugaban kwamitin harkokin addinin Musulunci, Alhaji Hammed Afolabi Bakare shi ya jagoranci raba kayan tallafin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ekiti - Shugabannin Musulmai a jihar Ekiti sun kwarara yabo ga fitaccen attajiri Aliko Dangote.

Shugabannin sun yabawa Dangote kan irin taimako da ya ke yi a jihar wurin amfani da Gidauniyarsa.

Dangote ya gwangwaje Musulmai da kayan abinci
Aliko Dangote ya sha ruwan yabo daga al'ummar Musulmai kan kayan tallafi. Hoto: Dangote Foundation. Asali: Facebook

Wane alkairi Dangote ya yi ga Musulmai?

Gidauniyar ta yi wa al'ummar Musulman jihar abin alkairi ta bangaren kayan abinci da sauransu musamman a lokacin Ramadan, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin ba da tallafin, Gidauniyar ta raba buhunan shinkafa akalla 10,000 ga dukkan ƙananan hukumomi 16 da ke fadin jihar.

Har ila yau, Gidauniyar ta kara tsawon hannu inda ta ba Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar tallafi na musamman.

Kwamitin harkokin Musulunci ya yabawa Dangote

Shugaban kwamitin harkokin addinin Musulunci a jihar, Alhaji Hammed Afolabi Bakare ya ce tallafin ya zo a dai-dai lokacin da aka fi buƙata.

Afolabi Bakare wanda ya jagoranci rarraba kayan abincin ya ce duk da matsalolin da aka samu an yi nasarar raba kayan inda ya kamata.

Ya ce tallafin ya kara rage ratan da ke tsakanin masu hali da marasa karfi da kuma bude ido ga sauran masu arziki domin yin koyi da shi.

Har ila yau, ya ce hakan zai karawa Musulmai da wadanda ba Musulmai ba son taimakawa al'umma.

Dangote ya koka da faduwar Naira

A wani labarin, Attajiri Aliko Dangote ya bayyana irin matsalar da kamfanoninsa ya samu yayin da darajar Naira ta karye a Najeriya.

Dangote ya ce 2023 ce shekara mafi muni a wurinsu da sauran masu kamfanoni inda suka rasa makudan kudin shiga.

Ya ce hakan ya tilasta su rashin iya biyan kudi ga masu hannun jari inda ya ce yana da tabbacin za su shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

People are also reading