Home Back

Chelsea ta ci gaba da neman Duran, Arsenal da Man United na gogayya kan Zirkzee

bbc.com 2024/7/8
Joshua Zirkzee

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta sake farfado da sha'awarta ta siyan Jhon Duran, Juventus na gab da siyan Douglas Luiz, Levi Colwill ya ci gaba da zawarcin Bayern Munich.

Chelsea ta sake farfado da zawarcin dan wasan Aston Villa da Colombia Jhon Duran, mai shekara 20. (Telegraph)

Juventus na ci gaba da tattaunawa don dauko dan wasan Brazil Douglas Luiz mai shekara 26 daga Aston Villa. (Sky Sports)

Har yanzu dan wasan baya na Chelsea da Ingila Levi Colwill, mai shekara 21, yana son komawa Bayern Munich duk da sha'awar da suke yi ta daukar dan wasan baya na Jamus da Bayer Leverkusen Jonathan Tah mai shekaru 28 da. (Sky Jamus), tuni dai Bayern ta fara tattaunawa da Leverkusen a kan Tah. (Bild)

Colwill dai ya zauna a Chelsea kuma kungiyar ba ta son siyar da shi. (Standard)

Manchester United na shirin yin gogayya da Arsenal wajen zawarcin dan wasan Bologna dan kasar Holland Joshua Zirkzee, mai shekara 23, wanda aka yi wa kudi fam miliyan 34. (Metro)

Arsenal na fuskantar kalubale na ci gaba da rike dan wasan gaban Denmark dan kasa da shekaru 17, Chido Obi-Martin, mai shekara 16, wanda Bayern Munich ke nema. (Metro)

Manchester United ta fitar da jerin sunayen wadanda take fatan za su kasance yan wasan gabanta, da suka hadar da dan wasan Brentford na Ingila Ivan Toney, mai shekara 28, da dan wasan Lille da Canada Jonathan David, mai shekara 24, da ake ta zuzutawa (ESPN)

West Ham ta yi wa dan wasan bayan Ingila Ben Johnson, mai shekara 24, tayin sabunta kwantiraginsa da shekaru biyar. (Athletic)

Fulham ce ke kan gaba wajen neman Silas Katompa Mvumpa, mai shekara 25, daga Stuttgart, inda dan wasan na JD Kongo ya kai fam miliyan 15. (HITC)

Arsenal na son siyar da dan wasan bayanta dan Scotland Kieran Tierney a wannan bazarar ko da ba za ta maida kudinsa ba. Ana ganin idan kungiyar ta samu fam miliyan 15 ma za ta iya sayar da dan wasan mai shekaru 27. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Jamus Pascal Gross, mai shekara 32, yana tattaunawa da Brighton kan tsawaita kwantiraginsa. (Athletic)

Crystal Palace da Ipswich da Southampton na fafatawa kan dan wasan bayan Rochdale dan kasar Wales mai shekaru 18, George Nevett. (HITC)

People are also reading