Home Back

Tattalin Arzikin Afrika Na Habaka Cikin Sauri

leadership.ng 2024/4/28
Tattalin Arzikin Afrika Na Habaka Cikin Sauri

Tattalin arzikin kasashen Afrika na ci gaba da habaka cikin gaggawa duk kuwa da wasu tarin matsalolin da nahiyar ke fama da su da suka hada da tsadar rayuwa da sauyin yanayi da tashe-tashen hankula da karancin abinci har ma da basuka.

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika Dokta Akinwumi Adesina ne, ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da jakadu da wakilan bankin da aka saba gudanarwa duk shekara.

“An yi hasashen cewa, Afrika za ta samu kaso 11 daga cikin 20 na kasashen duniya da ke tattalin arziki mai habaka cikin sauri a cikin wannan shekara ta 2024,” in ji Adesina.

Wani fashin baki kan hanyoyin bunkasar tattalin arziki a sassan Afrika ya nuna cewa, Najeriya ta samu habakar ma’aunin tattalin arzikinta da kashi 3.46 a cikin kashin karshe na shekarar da ta gabata kamar yadda shugaban na Bankin Afrika ya yi karin haske.

Tattalin arzikin Ghana kuwa ya samu jan kafa da kashi 2 a kashi na uku na shekarar bara, matsalar da ke da nasaba da koma-bayan da ma’aikatun kasar suka samu.

Kenya ta samu habakar tattalin arziki da kashi 5.9 a kashi na uku na shekarar 2023 sakamakon farfadowar bangaren noma.

 
People are also reading