Home Back

Sojoji sun dakile harin ƴanta’adda a ƙauyen Damba Dikko, sun kashe mutum biyu

premiumtimesng.com 2024/4/28
Sojoji sun  kashe Ƴan ta’adda 60, sun kama 50 a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya cikin makonni uku

Sojojin Najeriya, a ranar Laraba, sun yi nasarar dakile harin ƴanta’adda a kauyen Damba Dikko da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.

Nwachukwu ya ce maharan sun kai wa al’ummar garin hari ne da don karbar haraji daga mutanen kauyen.

Sai dai ya ce sojojin sun yi gaggawar dira wannan ƙauye a lokacin da aka sanar da su zuwan ƴan ta’addan ƙauyen tare da yin artabu da maharan.

Ya ce sojojin sun kashe biyu daga cikin maharan tare da kubutar da wasu mutanen kauyen biyu da maharan suka yi garkuwa da su.

Nwachukwu ya ce mutanen kauyen da aka ceto da suka samu kananan raunuka sun samu kulawar jami’an bayar da agajin gaggawa na sojojin Najeriya.

Nwachukwu ya kara da cewa a wannan rana sojojin sun ceto wasu mutane hudu da wasu gungun masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su a jihar Edo.

Nwachukwu ya yabawa jama’a bisa hadin kan da suke baiwa sojoji da sauran jami’an tsaro wajen yaki da kalubalen tsaro a kasar.

Ya kuma kara musu kwarin guiwa da su ci gaba da taka tsan-tsan tare da gaggauta kai rahoton duk wani yunkuri da ake kyautata zaton na ƴanta’adda ne ga jami’an tsaro da hukumomin da abin ya shafa.

 
People are also reading