Home Back

Sarautar Kano: Abba Hikima Ya Magantu Kan Sahihin Sarkin Kano, Ya Jero Dalilai

legit.ng 2024/7/5
  • Fitaccen lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya bayyana matsayar hukuncin sarautar da aka yanke a jiya Alhamis
  • Abba ya ce a mahangar shari'a, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ne sahihin sarki kamar yadda doka ta tabbatar
  • Wannan martani na Hikima na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci a jiya Alhamis 20 ga watan Yunin 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya yi martani kan dambarwar sarautar jihar Kano.

Abba ya ce babu wani rudani kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya inda ya ce komai a bayyane yake.

Abba Hikima ya fadi sahihin Sarkin Kano a yanzu
Fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin Sarki. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Hikima, Masarautar Kano. Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hikima wanda dan asalin jihar Kano ne ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024.

Lauyan ya ce a yanzu sahihin Sarkin Kano a mahangar doka shi ne Aminu Ado Bayero saboda kotu ta yi fatali da matakan Gwamna Abba Kabir.

Ya ce kafin wannan lokaci kotun ta ba da umarni kan matakin da gwamnan ya dauka bayan mayar da Muhammadu Sanusi II.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading