Home Back

Za’a kama duk wanda aka samu da makamai a gidan sa – Ƴan sandan Kano

dalafmkano.com 2 days ago

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Salman Garba Dogo, ya bada umarnin yin maganin dukkanin wanda ya fito harkar Daba, tare da dukkan wanda ya tsaya musu, domin kare lafiya da dukiyoyin al’umma.

Kwamishinan ya kuma ce duk wanda aiki ya biyo ta kan sa ba za’a ɗaga masa ƙafa ba, domin kuwa an bai wa ƴan sanda kayan aiki da zasu gudanar da aikin a cikin nasara.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya a shafin sa na sada zumunta.

Ya kuma ce yanzu haka ana farautar duk mutumin da aka samu da muggan makamai, irin su Fate-fate, da Ɗan Bida, da Gariyo, da kuma makami mai nau’in Switzerland, a cikin gidansa za’a kamashi.

Rundunar ƴan sandan Kano, ta kuma buƙaci haɗin kan al’ummar jihar, domin samar da tsaro a garesu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da matsalar harkar Daba ta addabi al’umma musamman ma a sassan birnin Kano, al’amarin da al’umma ke ci gaba da neman ɗaukin mahukunta dan ganin an magance matsalar bisa yadda hakan ke sanadiyyar kashe rayukan mutane.

People are also reading