Home Back

Sudan: Yaki na kara kazancewa a El Fasher

dw.com 2024/7/1
Dattijo ya yi tagumi sakamakon kokoluwar yaki a Sudan
Dattijo ya yi tagumi sakamakon kokoluwar yaki a Sudan

Masu sa ido da sauran masana sun nuna fargaba kan kazancewar yaki da ke alamta makamancin yanayin da aka taba fuskanta a yakin Darfur a shekarar 2003, sakamakon tabarbarewar al'amura baki-daya, a dalilin kawanyar da dakarun RSF suka yi wa birnin El Fasher mai mutane miliyan daya da rabi a yankin Darfur na tsawon watanni biyu, ba tare da barin al'ummar yankin sun numfasa ba.

A makon da ya gabata an kashe mutane 226 a garin, yayin da a watan Afirilun 2024 kuma mutane dubu dari da talatin (130) suka tsere daga garin a cewar Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce daga fara yakin a cikin watan Afirilun 2023 zuwa yanzu, kididdiga ta nuna cewa mutane dubu goma sha shida ne suka halaka, dubu talatin da uku kuma suka samu raunuka, yayin da miliyan tara suka tsere daga gidajensu, miliyan biyar daga cikinsu kuma na fuskantar matsananciyar yunwa.

Wasu mazauna El Fasher da DW ta tattauna da su, sun ce babu abin da ke ransu face taraddadi da fargabar rashin sanin me zai faru da su, kamar yadda wani mai suna Taj Alseer Ahamed ya fada yana mai cewa ''Ba mu san me za mu yi ba a wannan lokaci na yaki, shin ko ta yaya ma za mu kaucewa harsasai da sauran makamai da ake harbawa, ga shi ma duk 'yan uwanmu sun tarwatse sun bar gidajensu, babu abinci babu ruwa, babu kudi, hasali ma bama iya bacci, tunaninmu da nutsuwarmu sun dabarbarce kwata-kwata. An rufe shaguna, kuma a haka ma wasu mutane dauke da makamai da ba mu sansu ba sun ce mu fice daga gidajenmu, yaya ake so mu yi da rayuwarmu''.

Karin bayani : RSF za ta bude hanyar fita daga birnin Darfur

Kungiyar kare hakkin 'dan adam ta Human Rights Watch ta nemi masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar matakin kawo karshen yakin, kuma babban jami'inta na bincike a Afirka Mohamed Osman ya ce "Halin da El Fasher ke ciki ya yi muni matuka, an kashe daruruwan mutane, dubbai sun bar muhallansu, rayuwa ta yi tsanani ga wadanda suka rage a garin. Bukatar agaji ta karu sosai, kuma yakin ya hana shigar da kayan tallafin ga al'umma, wannan ya saba da dokokin yaki, saboda haka muna bukatar ganin daukar matakan gaggawa tare da matsin lamba ga bangarori biyun da ke gwabza fadan''.

Karin bayani : Yakin Sudan ya dauki hankalin Jaridun Jamus

Ita kuwa cibiyar da ke binciken al'amuran yau da kullum da ke faruwa a duniya ta GIGA Institute for Global Area Studies, mai mazauni a nan Jamus ta sanar da cewa ta gano yadda RSF din ke kona komai na al'umma tare da tilastawa mutane shiga cikinta domin dafa mata a yakin, wanda shi ne salon da magabatansu 'yan tawayen Janjaweed suka yi amfani da shi a yakin Darfur na shekarar 2003, kuma a a yanzu ma 'yan ana tursasawa manoma shiga cikinsu don yin yaki, inda suke kashe mazan da suka nuna tirjiya, mata kuma ana yi musu fyade da bautar da su'', kamar yadda jami'ar cibiyar Hager Ali ta tabbatar.

Yanzu haka babban fatan gwamnatin sojin Sudan shi ne kwace iko da Darfur, da mafi yawancinsa ke karkashin ikon RSF, tare da samun damar isar da kayan agaji ga al'ummar yankin da ke cikin tsananin matsin rayuwa.

People are also reading