Hajj 2024: Bayan Mutuwar Tawakaltu, Wani Alhajin Najeriya Ya Mutu Yana Ibada a Saudiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Makka, Saudiya - Wani Alhajin Najeriya da ke gudanar da aikin Hajji ya rasu a kasar Saudiyya. An ce marigayin dan asalin jihar Kebbi ne.
Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, Faruku Aliyu-Enabo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Lahadi.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa marigayin Muhammad Suleman, ya rasu ne a ranar Lahadi bayan gajeruwar jinya a garin Makkah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan rasuwar wata Hajiya mai suna Tawakaltu Alako wadda ita ma ‘yar asalin jihar Kebbi ce.
Alako ta rasu ne a ranar Asabar bayan ta yanke jiki ta fadi otal din da ta ke zama a Makkah.
Aliyu-Enabo ya bayyana cewa an yi jana’izar Suleman kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, in ji rahoton jaridar The Cable.
“Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma an yi sallar jana’izarsa a masallacin Harami (Ka’aba).
“A madadin gwamnatin jihar Kebbi, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa, alhazan Kebbi da daukacin jihar baki daya.
InnalilLahi: An shiga jimami yayin da ɗan Majalisa mai-ci ya rasu a Adamawa
"Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma jikansa da rayukan dukkan Musulmin da suka rasu."
- In ji Aliyu-Enabo.
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya nada sabon Amirul Hajji da zai jagoranci maniyyatan Kano zuwa aikin Hajjin bana a Saudiya.
Abba ya nada mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam a matsayin Amirul Hajj na Kano a bana yayin da alhazan jihar za samu kyautar $500 kowanne.
Asali: Legit.ng