Home Back

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

dalafmkano.com 2024/5/19

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

People are also reading