Home Back

ARAFAT: Masu Da’awa 100 aka tura Hajji don faɗakar da Alhazan Kebbi – Sheik Umar-Wasagu

premiumtimesng.com 2024/7/1
ARAFAT: Masu Da’awa 100 aka tura Hajji don faɗakar da Alhazan Kebbi – Sheik Umar-Wasagu

Na’ibin limammin Babban masallacin Juma’a da ke Birnin Kebbi, Sheikh Kabir Umar-Wasagu ya bayyana cewa masu Da’awa akalla 100 ne gwamnatin jihar ta aika Hajji bana domin faɗakar da Alhazan jihar.

A wata sanarwa wacce Kakakin gwamnan jihar Kebbi ya fitar ranar Alhamis, ta bayyana cewa dalilin aiakwa da masu da’awa haka shine don a wayar wa Alhazan jihar kai game da abubuwan da ya kamata su yi a lokacin aikin Hajjin.

Sheikh Umar-Wasagu wanda shima ya na cikin kwamitin masu da’awan ya bayyana irin haka a kwaryakwaryar bita da aka yi wa alhazan jihar bayan sallar Azahar a garin Makka ranar Alhamis.

” Dalilin da ya sa muka taho da masu wa’azi har 100 shine don a samu wadanda za su rika tunatar da Alhazai a koda yaushe.

” Ko wacce mota muna so a saka akalla malami guda da zai rika yi musu wa’azi.

Daga nan sai ya hori alhazai su nuna dattaku da kamala a lokacin da ake shiga motocin da za a kaisu Muna, yana mai cewa babu wanda za a bari a lokacin tafiya.

Sannan ya yi kira ga alhazan su yi taka tsantsan da kula da ƴan damfara, yana mai cewa wasu na nan sun zo ne su damfare ba aikin suka zo na Allah da Annabi.

People are also reading