Home Back

Dillalin Raguna Ya Bayyana Abin da Ke Kokarin Hana Mutane Layya a Najeriya

legit.ng 2024/7/6
  • Magidanta sun koka kan tsadar kayan masarufi yayin da hidimar bikin babbar sallah ke kara ƙaratowa a tarayyar Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun fifita sayan kayan abinci a kan sayan raguna domin gabatar da ibadar layya
  • Masu sayar da raguna da magidanta sun bayyana ra'ayoyinsu kan halin da kasar ke ciki da kuma yadda suka fuskanci babbar sallah

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - A yayin da ake fuskantar sallar layya, yan Najeriya na cigaba da fuskantar tsadar kayan masarufi.

Magidanta da dama a birnin Jalingo da ke jihar Taraba sun fitita sayan kayan abinci a kan ragon yin yankar sallah.

Raguna layya
Tsadar rayuwa na kokarin hana mutane layya. Asali: Original

Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa tsadar abinci ne ke kokarin hana mutane da dama gabatar da ibadar layya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsadar abinci: Magidanta sun koka kan layyah

Wani magidanci, Yakubu Adamu ya bayyana cewa a shekarar da ta wuce abinci bai yi tsada kamar na bana ba.

Yakubu Adamu ya ce a wannar shekarar yana da wahala ga talakawa su iya hada sayan abinci da ragon layya.

Har ila yau, wani magidanci Yakubu Haruna ya ce a yanzu haka ya fifita samar da abinci a gidansa a kan sayan ragon sallah.

Ya ce tanadin abinci ne abu na farko da ya kamata magidanta su mayar da hankali a kai sai idan an samu dama kuma a sayi rago.

Kasuwar raguna ta yi baya da sallah

Wani dillalin raguna, Sa'idu Lawal ya koka kan yadda ciniki ya yi baya a wannar shekarar duk da kokarin da suke wajen jawo masu sayayya.

Sa'idu Lawal ya ce ko da mutane sun zo sayan raguna suna sayan ƙanana ne, mutane kaɗan ne ke iya sayan manya.

Dillalin ya kuma bayyana cewa tsadar kayan abinci ne ya hana mutane da dama zuwa kasuwa sayan ragunan sallah a wannan karon.

Layyah: An yiwa malamai kyauta a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ba malaman addinin Musulunci gwaggwaɓar kyauta domin hidimar sallar layya.

Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan harkokin addini na jihar Sokoto, Dakta Jabir Sani Mai Hula ne ya bayyana lamarin ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

People are also reading