Home Back

Pedri ba zai buga wa Sifaniya sauran wasannin Euro 2024 ba

bbc.com 2024/8/21
Pedri

Asalin hoton, Getty Images

Pedri ba zai buga wa Sifaniya, sauran wasannin Euro 2024 ba, bayan da ya ji rauni a gwiwa a karawar da suka doke Jamus 2-1 ranar Juma'a.

Mai shekara 21 ya bar filin yana kuka tun farkon fara wasan, bayan da ya yi taho mu gama da ɗan ƙwallon Jamus, Toni Kross.

To sai dai Pedri zai ci gaba da jinya a tawagar Sifaniya a Jamus har bayan kammala Euro 2024, in ji wata sanarwa da hukumar ƙwallon kafar kasar ta fitar.

Kross, wanda ya yi ritaya daga taka leda, bayan da aka fitar da Jamus daga Euro 2024 ranar Juma'a, ya yi ban kwana da magoya baya, ya kuma nemi afuwar Pedri.

Raunin da Pedri ya ji ya sa koci, Luis La Fuente ya canja shi da Dani Olmo, wanda shi ne ya ci Jamus ƙwallon farko, sannan ya bayar da na biyu aka zura a raga.

Kenan Sifaniya za ta fuskanci Faransa a daf da karshe ranar Talata 9 ga watan Yuli.

Faransa ta kai daf da karshe, bayan da ta yi nasara a kan Portugal a bugun fenariti, bayan da suka tashi ba ci.

To sai dai Sifaniya za ta buga wasan gaba ba tare da Robin Le Normand ba, wanda ya karbi kati gargaɗi na biyu a gasar da kuma Dani Carvajal, wanda aka bai wa jan kati a filin wasa na Stuttgart.

An yi laifi 38 a karawar da rafli, Anthony Taylor ya busa, inda aka bai wa Jamus katin gargadi takwas, ita kuwa Sifaniya ta karɓi shida da jan kati ɗaya.

An tashi fafatawar 1-1 daga nan aka yi karin lokaci, inda Sifaniya ta ci ƙwallo na biyu ta hannun Mikel Merino da hakan ya kai ta daf da karshe a Euro 2024.

People are also reading