Home Back

Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri

leadership.ng 2024/4/29
Ya Kamata CBN Ya Sanya Hoton Obasanjo A Jikin Sabbin Kudin Da Za A Sauya Wa Fasali

‘Yan adawa na shirin kafa sabuwar jam’iyyar domin kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a 2027.

Gabanin 2027, majiyoyi sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar, ya hada kai da wasu ‘yan majalisa domin kafa sabuwar jam’iyya.

Sun kara da cewa Atiku ya kaddamar da tawaga mai karfi domin jagorantar kafa sabuwar jam’iyyar adawa da za ta fara aiki kafin zaben 2027, inda yake tunanin cewa jam’iyyar za ta iya kwace mulki daga wurin APC.

Majiyoyin sun ce tsohon mataimakin shugaban kasan ya hada kai da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda ya nemi shugabancin majalisan dattawa bai samu ba.

Haka kuma shugaban kungiyar sanatocin arewa (NSF), Abdul Ningi, zai shiga cikin wannan tawaga domin ya kasance sojon gona a zauren majalisa wajen tabbatar da sabuwar jam’iyyar.

A cewar masu sharhi kan al’amurar siyasa, wannan lamari na iya mammaita abun da ya faru a 2013, inda wasu gwamnoni da ‘yan majalisa suka yi wa PDP tawaye tare da yin aiki tare wajen kafa jam’iyyar APC wanda ta kwace mulki.

An dai kafa APC ne a watan Fabrairun 2013, sakamakon kwawancen jam’iyyu da suka hada da CAN, CPC, ANPP, APGA da kuma wani bangare na sabuwar PDP.

Atiku yana daga cikin wadanda suka jagoranci kafa jam’iyyar APC, inda ya tsaya takarar shugaban kasa a 2014, sai dai Muhammadu Buhari ya kayar da shi tun a zaben fitar da gwani.

Ya dai sake dawowa PDP, inda ya tsaya takara a 2019, sai dai kuma ya sha kaye a hannun Buhari. Sannan a zaben bara kuma, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kayar da shi.

Majiyoyin sun ce Atiku da sauran abokanansa suna kokarin maimaita abun da ya faru a 2013 na kafa sabuwar jam’iyyar kuma har da kwace mulki.

Ya ce, “Mun yi nisa kan wannan yarjejeniya. Mun tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mummunan hali fiye da na 2014 lokacin mulkin Goodluck Ebele Jonathan, shi ya sa muka yi wannan shiri na kafa sabuwar jam’iyyar domin kwace mulki daga wurin Tinubu.”

Wani sanata daga kudu ya ce mafi yawancin abokansa suna sane da yin shiri domin mulki ya dawo arewa idan har suka samu nasarar raunata gwamnatin Tinubu a 2027.

Ya ce, “Mun san irin shirin da ake yi. Muna kallon su ne kwai. Suna ta yin siyasa wajen kawo rudani a jam’iyyarmu wanda za a ruruta wutar fada a tsakaninmu da bangaren shugaban kasa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

Ningi, wanda yake wakiltar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa ya shaida wa sashin Hausa na BBC cewa sanatocin arewa za su yaki shugaban kasa.

Ya ce, “Lallai ba za su yaki gwamnati ba kamar yadda ‘yan adawa ke yi ba. Amma dai wannan irin sakamako ne ya dace da gwamnatin da muke da ita. Wadannan shugabannin da suke gallaza mana ba su muka zaba ba.

“Mun kawo bambance-bambancen addini da kabilanci wajen gudanar da sha’anin gwamnati. Sun kawo farfagandar cewa ba za a amince a kara bai wa Bahaushe ko Fulani shugabanci ba, saboda ba a samun zaman lafiya.

“Idan aka duba da idon basira za a ga cewa mafi yawan ‘yan adawa sun fito ne daga yankin arewa maso gabas da kuma arewa maso yamma. Amma an ki amincewa mu zama shugabannin ‘yan adawa a zauren majalisar dattawa ba.

“Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da muka ce za mu duba mu gani kan abubuwan da ke faruwa a karkashin kungiyar sanatocin arewa, wanda nake shugabanci a yanzu haka,” in ji shi.

Tags: Atiku

 
People are also reading