Home Back

Ci Gaban Kasar Sin Dama Ce Ta Bunkasar Duniya

leadership.ng 2024/6/29
Ci Gaban Kasar Sin Dama Ce Ta Bunkasar Duniya

Hukumomin kasa da kasa na ci gaba da bayyana kyakkyawan fatansu ga karkon da tattalin arzikin kasar Sin ke da shi, tare da bayyana hasashen ci gaban hakan a shekaru dake tare, suna masu bayyana imanin su ga manyan nasarorin da Sin din ke samu ta fuskar fadadar cinikayya, da kere-keren masanaantu, da daidaito a alkaluman raya tattalin arziki. Ko shakka babu, hakan na kara sanyawa sassan kasa da kasa kara jin karfin gwiwa game da tattalin arzikin Sin.

A tsawon shekaru, kasar Sin na ta daukar matakan dunkulewa, da kara kaimin farfado da tattalin arziki, da samar da sabbin damammaki ga kasashen duniya, musamman masu tasowa ta fuskar ingiza bunkasuwa tare, karkashin shirye-shirye daban daban, irin su dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC, da shawarar “ziri daya da hanya daya” da sauran su, ta yadda za a kai ga samar da duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil adama.

Hukumomi da cibiyoyin hada-hadar kudade na duniya, irin su bankin samar da ci gaba na Asiya, da Goldman Sachs, da Morgan Stanley da sauran su, duk sun daga mizanin hasashen da suka yi na ci gaban tattalin arzikin Sin a shekarar nan ta 2024. Hakan kuma manuniya ce ga yadda Sin din ta zamo muhimmiyar mai samar da daidaito, da ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya.

A zahiri take cewa Sin ta taka muhimmiyar rawa, wajen samar da hajoji bisa kyakkyawan farashi ga kasuwannin duniya a matsayinta na babbar cibiyar masanaantu. Tana kuma fadada shigo da hajojin sauran kasashe zuwa babbar kasuwarta mai dinbin jamaa. Kaza lika, matakin Sin na kara bude kofa, da gudanar da sauye-sauye masu inganci, sun kara fadada cudanyarta, da cin gajiya tare da sauran sassan kasa da kasa.

Yayin da Sin ke kara bude kofa ga waje, a daya bangaren tana kara zamanantar da kanta karkashin manufofin samar da ci gaba mai nagarta, inda masharhanta da dama ke ganin babbar kasuwar kasar mai yawan alumma da ta kai sama da biliyan 1.4, za ta ci gaba da bude sabbin babuka na ci gaba da kara farfadowa.

Duniya na kara shaida yadda kasar Sin ke ci gaba da raba damammakinta tare da sauran kasashe, ta yadda za a kai ga samun ci gaba mai dorewa, da nasarar dukkanin manufofin gina alummar duniya mai cin gajiyar hadin gwiwar bai daya.

People are also reading