Tumatur Ya Yi Tsada a Najeriya, Manoma Sun Bayyana Dalili
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fitar na cigaba da kawo tsadar kayan masarufi a kasuwannin Najeriya.
A kwanan nan an fara samun tsadar kayan miya a bangarori da dama na Arewaci da kudancin Najeriya.
Wasu manoma a jihar Bauchi sun bayyanawa jaridar Daily Trust dalilan da suka jawo karanci da tsadar tumatur a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu nomar rani a jihar Bauchi sun bayyana cewa karin kudin mai da kudin wuta suna cikin abubuwan da suka hana mutane da dama nomar rani a Najeriya.
Sun ce rashin nomar yadda ya kamata ya haifar da ƙarancin tumatur a kasuwanni wanda ya jawo tsadarsa sosai.
Shugaban masu nomar rani a jihar Bauchi, Alhaji Sani Abubakar ya ce dole farashin ya cigaba da tashi saboda matsaloli da dama.
Ya ce matuƙar ba a samo mafita ga abubuwan da suka jawo tashin farashin ba to dole zai cigaba da haurawa a kowace rana.
Shugaban manoman ya bayyana cewa tashin farashin ya shafi dukkan kayan miya da ake nomawa a rani.
A cewarsa, a bara sun sayar da buhun tattasai a N2,500 amma a yau saboda matsalolin tattalin arziki suna sayar da shi a N60,000 zuwa N80,000.
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya, ta ce ta janye tallafin wutar lantarki ne domin wadatar da wutar a Nijeriya nan da shekara uku masu zuwa.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce dole 'yan Nijeriya za su biyan kudin wuta da tsada.
Asali: Legit.ng