Home Back

Tumatur Ya Yi Tsada a Najeriya, Manoma Sun Bayyana Dalili

legit.ng 2024/7/5
  • A yayin da mafi yawan kayan masarufi suke kara tsada a Najeriya, kayan miya sun shiga sahun abubuwan da suka kara kudi
  • A gefe guda, farashin danyen tumatur ya yi tashin gauron zabi tare da wahalar samuwa a mafi yawan kasuwannin Najeriya
  • Manoma a jihar Bauchi sun bayyanawa manema labarai abin da ya jawo karancin tumatur da tsadarsa a kasuwannin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fitar na cigaba da kawo tsadar kayan masarufi a kasuwannin Najeriya.

A kwanan nan an fara samun tsadar kayan miya a bangarori da dama na Arewaci da kudancin Najeriya.

Tsadar tumatur
Manoma sun ce karin kudin mai ya jawo tashin farashin tumatur. Hoto: Hassan Bahaushe Gombe Asali: Facebook

Wasu manoma a jihar Bauchi sun bayyanawa jaridar Daily Trust dalilan da suka jawo karanci da tsadar tumatur a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin tsadar tumatur a Najeriya

Masu nomar rani a jihar Bauchi sun bayyana cewa karin kudin mai da kudin wuta suna cikin abubuwan da suka hana mutane da dama nomar rani a Najeriya.

Sun ce rashin nomar yadda ya kamata ya haifar da ƙarancin tumatur a kasuwanni wanda ya jawo tsadarsa sosai.

Karin haske daga shugaban manoma

Shugaban masu nomar rani a jihar Bauchi, Alhaji Sani Abubakar ya ce dole farashin ya cigaba da tashi saboda matsaloli da dama.

Ya ce matuƙar ba a samo mafita ga abubuwan da suka jawo tashin farashin ba to dole zai cigaba da haurawa a kowace rana.

Yadda farashin kayan miya ya tashi

Shugaban manoman ya bayyana cewa tashin farashin ya shafi dukkan kayan miya da ake nomawa a rani.

A cewarsa, a bara sun sayar da buhun tattasai a N2,500 amma a yau saboda matsalolin tattalin arziki suna sayar da shi a N60,000 zuwa N80,000.

Daliln karin kudin wuta

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya, ta ce ta janye tallafin wutar lantarki ne domin wadatar da wutar a Nijeriya nan da shekara uku masu zuwa.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce dole 'yan Nijeriya za su biyan kudin wuta da tsada.

Asali: Legit.ng

People are also reading