Home Back

Yunwa Ta Sa Muka Kashe Wani Yaro Don Samun Na Abinci  – Samari

leadership.ng 2024/6/29
Yunwa Ta Sa Muka Kashe Wani Yaro Don Samun Na Abinci  – Samari

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, Husseini Suleiman da Muktar Mohammed, sun amsa laifin kashe wani yaro ɗan shekara shida a Ganye da ke jihar Adamawa, domin samun kuɗin abinci. Wadanda ake zargin ƴan asalin ƙauyen Bashin ne da ke jihar Taraba, sun aikata laifin kuma sun shaida wa ƴansanda cewa sun yi garkuwa da Ebuka Godwin ne domin karbar kuɗi daga hannun iyayensa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin Almajirai ne a wata makaranta da ke yankin, sun ƙera bindigu na bogi daga katako domin yin garkuwa da Ebuka.

Sun buƙaci a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 10 da kuma ƙarin Naira 152,000 domin ciyar da su, wanda mahaifin wanda abin ya shafa ya biya. Bayan karbar kuɗin ne waɗanda ake zargin suka shake yaron har ya mutu kuma suka binne gawarsa.

Daga nan ne waɗanda ake zargin suka tsere inda suka yi amfani da kuɗin wajen siyan sabbin wayoyi.

People are also reading