Home Back

Saurayi Ya Raunata Budurwa Tare Da Barazanar Kisa Saboda Ta Ki Son Sa A Maiduguri

leadership.ng 2024/5/4
Masallata Sun Kuɓuta Daga Harin Ƙunar Baƙin Wake A Jihar Borno

Wani saurayi, Saleem Ibrahim, da ya kamu da tsananin kaunar wata budurwa, Hauwa Abatcha Ngala dukkansu daliban Jami’ar Maiduguri, ya yi mata mummunan rauni a kai saboda kin amincewa da soyayyarsa.

Kamar yadda majiyar Zagazola Makama, wani masani a kan fannin yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi ta ruwaito, an ce Saleem ya dade yana kokarin tilasta wa Hauwa son sa, amma bai samu hakan ba, domin Hauwa ta yi iya kokarinta wajen cusa sa shi a zuciyarta abin ya gagara, har dai ta yanke hukuncin cewa duk irin kokarin da za ta yi na shawo kan zuciyarta ta so Saleem Ibrahim ba zai yiwu ba don ba ta jin son sa a ranta ko miskala zarratin.

Sakamakon haka, Hauwa ta nemi hanyoyin da za ta rabu da Saleem salim-alim don ta huta da takurawar da yake mata a kokarinsa na ganin ta so shi amma sai ya ci gaba da nuna mata naci.

Duk yadda ta yi kokarin kubutar da kanta daga abubuwan da ya ke yi mata da sunan lallashinta ta so shi, amma hakan bai kara komai ba sai kinsa a ranta.

Saleem ya ki hakura har dai ya fara yi mata mummunar barazana ciki har da cewa zai iya kashe ta idan har ba ta karbi soyayyarsa.
An ruwaito cewa, ya gaya mata ko dai ta karbi soyayyarsa ko kuma ta gamu da gamonta.

“Zan iya kashe ki kuma babu abin da zai faru,” Saleem ya yi mata kashedi kamar yadda aka ruwaito.

Wannan al’amari ya jefa Hauwa cikin tsananin bacin rai, inda ta zauna cikin wannan hali har zuwa ranar Litinin, 26 ga Fabrairu, 2024.

A ranar Litinin ta makon jiya, da misalin karfe 8:30 na dare Saleem Ibrahim ya tare Hauwa Abatcha Ngala inda ya buge ta da wani karfe har sau biyu ta fadi nan take ta suma, jini na ta zuba.

A maimakon ya yi duk wani kokari na ceto rayuwarta, saboda son da ya ke mata, kawai sai ya gudu ya bar ta nan tare da ‘yan uwanta, wadanda suka yi kokarin ceto rayuwarta ta hanyar kai mata agajin gaggawa.

Bayan ta farfado ne, ’yan uwanta suka kai rahoton lamarin ga ‘yansanda a daren wannan rana.

A dalilin haka ciki wannan dare ‘yan sa kai na JTF suka kama Saleem Ibrahim tare da mika shi ga ‘yansanda da ke ofishin Dibision na Gomari.

Sai dai kuma a ranar Juma’a 1 ga Maris, 2024, wato kwana uku da faruwar lamarin tare da kama shi, ‘yansanda sun saki Saleem bisa zargin sa hannun wasu ‘yan siyasa, ba tare da daukar wani mataki na nuna cewa dokar ta kama shi da laifi ba.

Bayan ‘yansanda sun sako Saleem, sai ya shiga shafinsa na Facebook ya aika wa Hauwa sako na sirri yana yi mata ba’a, yana mai cewa “Na na fi karfin na yi barazana a banza, duk abin da na ce zan aikata sai na yi kuma ba abin da zai faru. Na rantse da Allah, talaka ne kawai za ki ja da shi ki ci riba a kansa amma ba mutumin da ke ji da kansa kamar Saleem ba.

“Ku talakawa ba ku da gata domin ba ku da komai balle ku yi nasara a kaina. Idan kuwa har kuka yi nasara a kan wasu, na rantse da Allah Madaukakin Sarki ba za ku taba yi a kaina ba, domin muna da kudi, Hukumomin Tsaro, ‘Yan Siyasa, da Jami’an Gwamnati duk suna tare da mu. Sai dai kawai ki yi alfahari da ‘yan’uwanki, don a ci gaba da shari’ar, mu ga wane ne ke da rinjaye.”

‘Yan uwan da ransu ya baci bisa ga matakin da ‘yansandan suka dauka, sun sake shigar da kara a shalkwatar ‘yansandan Jihar Borno da ke Maiduguri, a ranar Asabar 2 ga Maris, 2024, musamman ma da ya yi zargin cewa zai kashe ta, kuma babu abin da zai faru domin shi da ne na masu hannu da shuni, wanda hakan ya fusata su.

Hakan ya sa aka sake kama Saleem tare da tsare shi tsawon mako guda a hannun ‘yansanda, amma ana zargin an sake shi kamar yadda ‘yansanda suka shaida wa iyalan cewa Sakataren gwamnatin Jihar Borno, Honarabul Bukar Tijjani ya bayar da umarnin a sake shi sannan kuma a yi watsi da karar ba tare da daukar wani mataki a kansa ba duk da ya yi wa Hauwa rauni mai tsanani na jiki da na zuciya.

Kwatsam sai ga ‘yan uwan Hauwa suka ci karo da Saleem yana yawo a titin Maiduguri cikin walwala kamar kowane dan kasa mai bin doka da oda, maimakon a ce yana hannun ‘yansanda an gurfanar da shi a gaban kotu.

Dangin Hauwa da ba su hakura ba, suka sake shigar da sabuwar kara a ofishin kwamishinan ‘yansandan Jihar Borno, (CP Yusuf Lawan) a ranar Talata, 12 ga Maris, 2024, inda suka bukaci a yi adalci a shari’ar.
Sakamakon haka ‘yansanda sun sake kama Saleem Ibrahim. A wannan karon, ‘yansanda sun gayyaci wacce lamarin ya shafa wato Hauwa kuma suka dauki rahotonta.

Daga nan ne ‘yansandan suka hada rahoto kan lamarin tare da mika shi ga ma’aikatar shari’a ta Jihar Borno.

Sai dai kawo yanzu babu wanda ya tuntubi Hauwa ko danginta, duk da Saleem ya furta cewa ya aikata laifin da kuma barazanar kashe ta.

Jummai Mshelia, Ko’odinetar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) ta Borno, ta yi Allah-wadai da faruwar lamarin inda ta ce wannan ba komai bane illa rashin hankali, ta kuma bukaci a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya zama izna ga sauran masu aikata laifin.

Ta ce: “Mu a matsayinmu na masu kare hakkin bil’adama, hukumarmu ta kai kara ga kwamishinan ‘yansanda wanda ya bayar da umarnin a kama wanda ake zargin nan take. Muna yaba wa ’yansanda saboda saurin daukar mataki.

“An shaida mana cewa an rubuta karar zuwa ma’aikatar shari’a don neman shawararsu. Yayin da muke jiran martanin sashen, muna so mu tabbatar wa jama’a cewa za a bi diddigin shari’ar har sai mun tabbatar da an yi adalci.”

Ta shawarci jama’a da su rika kai rahoto ga hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa ko kuma wata hukumar tsaro idan wannan ta faru domin kawar da miyagun laifuka a cikin al’umma.