Home Back

Saudiya Za Ta Shiga Gasar Sarauniyar Kyau Ta Duniya? Gaskiya Ta Bayyana

legit.ng 2024/5/12
  • Masu shiryar gasar fitar da sarauniyar kyau ta duniya, Miss Universe, sun ce babu Saudiya a jerin kasashen da suka shiga gasar ta bana
  • Wannan na zuwa ne bayan da wata jarumar tallace-tallace, Rumy Alqahtani ta sanar da cewa ita ce za ta wakilci Saudiya a gasar
  • Sai dai mahukuntan gasar sun ƙaryata wannan ikirari na Alqahtani, inda suka ce har yanzu Saudiya ba ta tantance wakiliya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Masu shirya gasar Miss Universe sun musanta rahotannin da ke cewa Saudiyya na shirin shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya a karon farko.

Masu shirya gasar sarauniyar kyau ta duniya sun magantu shigar Saudiya gasar ta bana
Miss Universe ta karyata ikirarin cewa Saudiya ta shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya. Hoto: Rumy Alqahtani Asali: Instagram

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Miss Universe wata gasa ce da ake shirya wa domin zabar mace mafi kyawu ta duniya.

"Zan wakil wakilci Saudiya" - Alqahtani

A watan da ya gabata, Rumy Alqahtani, jarumar tallace-tallace daga Saudiya, ta bayyana cewa za ta wakilci kasarta a gasar sarauniyar kyau ta shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alqahtani ta ce kasarta (Saudiya) za ta shiga gasar Miss Universe ta bana a karon farko a tarihin kasar.

"Ina matukar jin dadi da shiga cikin gasar Miss Universe 2024. Wannan shine karo na farko da Saudiya ta shiga gasar."

Rumy Alqahtani za ta wakilci Saudiya?

Amma a cikin wata sanarwa, masu shirya gasar Miss Universe sun bayyana ikirarin Alqahtani a matsayin "karya da yaudara".

Sanarwar ta ce har yanzu Saudiya ba ta cikin kasashen da aka tabbatar da cewa za su shiga gasar zaben sarauniyar kyau ta duniya ta bana.

Ko da yake, sanarwar ta kara da cewa kasar na fuskantar "tsattsauran tsarin tantancewa" domin zabar 'yar takarar da ta dace.

Rahotanni sun bayyana cewa an shirya gudanar da gasar Miss Universe na 2024 a Mexico a watan Satumba.

An zabi sarauniyar kyau ta Najeriya

Idan ba a manta ba, a shekarar 2021, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata matashiya 'yar jihar Kano, Shatu Garko ta lashe kambun sarauniyar kyau ta Najeriya.

As gasar karo na 44, an ga hotunan Shatu Garko sanye da Hijabi kasancewarta Musulma wacce ke da shekaru 18 a lokacin.

Asali: Legit.ng

People are also reading