Kungiyar G7 ta iyakance farashin man Rasha don hana ta samun kudi
Asalin hoton, Getty Images
Sa'o'i 3 da suka wuce
Kawayen kasashen Yamma sun amince a iyakance farashin mai da Rasha take sayar wa kasashen waje da ake sufurinsa ta teku.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa tare da Australia kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya sun ce amince da farashin dala 60 a kan kowace gangar mai da Tarayyar Turai ta kayyade a ranar Jumma 02-12-2022.
A sanarwar hadin gwiwa da kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 suka fitar sun ce matakin iyakance farashin zai fara aiki ne a ranar Litinin mai zuwa 05-12-2022 ko kuma nan bada jimawa ba.
Matakin na zuwa ne bayan da Tarayyar Turai ta amince da tsarin kuma bayan ta shawo kan Poland a kan ta goyi bayan matakin.
A karkashin tsarin kasashe ba za su iya biyan kudi fiye da dala 60 ba kan kowace gangar man fetur.
Manufar wannan tsarin ita ce hana Rasha samun riba daga man fetur da take fitarwa zuwa kasashen waje.
Kuma sun dauki matakan ganin cewa tsarin ba zai sa farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a kasuwanin duniya ba.
Sai dai wani mai sharhi a kan makamashi ya shaida wa BBC cewa ko shakka babu zai yi mumunan tasiri kan tattalin arzikin Rasha
Ya ce, ''tattalin arzikin Rasha da kasafin kudin kasar sun dogara ne kan man fetur a don haka duk wani matakin da za a dauka kan man fetur zai shafi tatttalin arzikin kasar da kuma wasu muradun Shugaba Putin
Sai dai a daya bangaren Rasha ta yi alla-wadai da matakin tana mai cewa ba za ta samar da mai ga kasashen da suka iyakance farashin man ba.
Haka kuma duk da cewa matakin zai yi wa tattaln arzikin Rasha illa amma ana ganin ba zai yi tasiri sosai ba saboda kasar za ta mayar da hanakli ne wajen sayar wa India da China da man fetur dinta wandanda a yanzu su ne kasashen da suka fi sayen man daga wurinta.