Home Back

Hajji: Saudiyya Ta Gargadi Kamfanonin Bogi Kan Aikata Damfara, Ta Jadadda Muhimmancin Biza Ga Mahajjata

leadership.ng 2024/6/2
Hajji: Saudiyya Ta Gargadi Kamfanonin Bogi Kan Aikata Damfara, Ta Jadadda Muhimmancin Biza Ga Mahajjata

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta Kasar Saudiyya ta gargadi mutanen da ke shirin gudanar da aikin Hajjin bana da su guji fada wa hannun ‘yan damfara musamman a kafafen sada zumunta.

Majiyar ta jaddada cewa dole ne duk mai son zuwa aikin hajji, ya samu takardar izinin aikin hajji mai inganci da mahukuntan Saudiyya suka bayar tare da hadin gwiwa da ofisoshin aikin hajji daga kasashensu.

Majiyar ta ce ma’aikatar ta sanya ido kan tallace-tallace da kamfen da ake yi a shafukan sada zumunta don gargadin mahajjata fada wa hannun mutanen bogi.

Hukumar ta yi kira ga mahajjata da su yi taka-tsan-tsan kada a damfare su.

Ma’aikatar ta yaba da kokarin da hukumar aikin hajji da umarah ta kasar Iraki ta yi na kame tare da rufe kamfanoni sama da 25 na bogi a shafukan sada zumunta.

Sun kuma yaba da hadin gwiwar kasashen duniya wajen yakar ‘yan damfara a yayin aikin hajji.

A cewar ma’aikatar, yana da muhimmanci samun biza ga wanda zai yi umarah, yawon bude ido, aiki, ziyartar iyali ko kuma gudanar da aikin Hajji.

Don haka ta shawarci mutane da su bi ka’idojin da hukumomin kasar suka gindaya, tare da kaucewa mu’amala da kamfanonin bogi.

Ma’aikatar ta kara da cewa ta sanya ido kan irin wadannan kamfanoni kuma ta shirya daukar mataki a kansu.

People are also reading