Home Back

Yajin Aikin NLC Ya Hana Jigilar Alhazai Zuwa Ƙasa Mai Tsarki? NAHCON Ta Faɗi Gaskiya

legit.ng 2024/7/3
  • NAHCON ta kwantar da hankalin maniyyata yayin da suka fara fargabar raaa aikin hajjin bana saboda yajin aikin ƴan kwadago
  • Hukumar ta bayyana cewa yajin aikin NLC ba zai dakatar da jigilar alhazai ba kuma idan Allah ya so za a kama kwashe su kafin 10 ga watan Yuni
  • Fatima Sanda Usara, mataimakiyar kakakin NAHCON ta ce a halim yanzu jirage uku zuwa shida ke tashi a kowace rana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ce yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shiga ba zai shafi jigilar maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki ba.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakiyar kakakin NAHCON ta ƙasa, Fatima Sanda Usara ta fitar bayan ƴan kwadago sun shiga yajin aiki ranar Litinin.

Jigilar alhazan Najeriya.
Yajin aiki ba zai hana jigilar maniyyata ba a Najeriya in ji NAHCON Hoto: NAHCON Asali: Facebook

Ta fahimci halin fargaba da maniyyatan suka shiga saboda yajin aikin, inda ta yi alƙawarin cewa za a kammala jigilar alhazai gab ɗaya kafin 10 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sanarwar ta bayyana cewa sama da alhazai 37,102 ne aka kwashe zuwa Saudiyya a halin yanzu.

"Jiragen da ke jigilar maniyyata na ci gaba da aikinsu kamar yadda aƙa tsara tun farko, an fara da awu uku kowace rana, amma yanzu ya ƙaru zuwa sawu shida a rana.

"A halin yanzun, hukumar NAHCON na tabbatar da an yi akalla sawu uku zuwa shida a kowace rana ya danganta da yadda aka tsara."

Ta ƙara da cewa kimanin maniyyata 13,176 har yanzun ba a kwashe su ba kuma wannan adadin zai ragu kafin ƙarewar jiya Litinin saboda wasu jiragen za su tashi.

"Ragowar adadin maniyyatan da har yanzu suke nan gida ya nuna cewa saura sawu ɗaya a jihohin kamar Kaduna, Gombe, Borno, Zamfara, Adamawa, Kebbi da Abuja mai ragowar alhazai 33."

"Jirgi ɗaya zai kwashe dukkan alhazan Kudu maso Kudu kuma za a samu ragowar kujeru. Ba a fara jigilar maniyyatan Taraba mai mutum 1,00 ba. Aiki ya yi nisa a Jigawa, Kwara, Neja da Sakkwato."

- Fatima Usara.

AHOUN ta roƙi NLC ta janye yajin aiki

A wani rahoton kuma kungiyar masu jigilar mahajjata ta kasa (AHOUN) ta yi kira na musamman ga kungiyar kwadago kan yajin aiki da ta shiga.

Cikin sakon ta kungiyar ta wallafa ta nuna cewa duk da muhimmancin yajin aikin ga rayuwar ma'aikata, yazo a lokacin da bai dace ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading