Yajin Aikin NLC Ya Hana Jigilar Alhazai Zuwa Ƙasa Mai Tsarki? NAHCON Ta Faɗi Gaskiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ce yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shiga ba zai shafi jigilar maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki ba.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakiyar kakakin NAHCON ta ƙasa, Fatima Sanda Usara ta fitar bayan ƴan kwadago sun shiga yajin aiki ranar Litinin.
Ta fahimci halin fargaba da maniyyatan suka shiga saboda yajin aikin, inda ta yi alƙawarin cewa za a kammala jigilar alhazai gab ɗaya kafin 10 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sanarwar ta bayyana cewa sama da alhazai 37,102 ne aka kwashe zuwa Saudiyya a halin yanzu.
"Jiragen da ke jigilar maniyyata na ci gaba da aikinsu kamar yadda aƙa tsara tun farko, an fara da awu uku kowace rana, amma yanzu ya ƙaru zuwa sawu shida a rana.
"A halin yanzun, hukumar NAHCON na tabbatar da an yi akalla sawu uku zuwa shida a kowace rana ya danganta da yadda aka tsara."
Ta ƙara da cewa kimanin maniyyata 13,176 har yanzun ba a kwashe su ba kuma wannan adadin zai ragu kafin ƙarewar jiya Litinin saboda wasu jiragen za su tashi.
"Ragowar adadin maniyyatan da har yanzu suke nan gida ya nuna cewa saura sawu ɗaya a jihohin kamar Kaduna, Gombe, Borno, Zamfara, Adamawa, Kebbi da Abuja mai ragowar alhazai 33."
"Jirgi ɗaya zai kwashe dukkan alhazan Kudu maso Kudu kuma za a samu ragowar kujeru. Ba a fara jigilar maniyyatan Taraba mai mutum 1,00 ba. Aiki ya yi nisa a Jigawa, Kwara, Neja da Sakkwato."
- Fatima Usara.
A wani rahoton kuma kungiyar masu jigilar mahajjata ta kasa (AHOUN) ta yi kira na musamman ga kungiyar kwadago kan yajin aiki da ta shiga.
Cikin sakon ta kungiyar ta wallafa ta nuna cewa duk da muhimmancin yajin aikin ga rayuwar ma'aikata, yazo a lokacin da bai dace ba.
Asali: Legit.ng