Home Back

MATSALAR ƘARANCIN ABINCI: Majalisar Ɗinkin Duniya za ta tallafa da Dala miliyan 11 domin ɗauki ga yankin Arewa maso Gabas

premiumtimesng.com 2 days ago
Idan abin ya gagara zamu tattara namu-inamu mu kuma kasar Kamaru – Mazauna Madagali
IDP children

A ƙoƙarin magance gagarimar matsalar wadatar abinci a yankin Arewa maso Gabas, Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa za ta tallafa da Dala miliyan 11, domin samar da abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Gabas.

Za a bayar da tallafin ne daga Asusun Gidauniyar Agajin Gaggawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNCERF).

Ƙaramin Sakataren Harkokin Agaji da Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Martin Griffin ne ya bayyana haka a ranar Asabar, a shafin sa na Tiwita, wato X.

Griffin ya ce ƙarancin abinci mai gina da jiki da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan na ƙara yin ƙamari sosai, yayin da ya ƙara da cewa matsalar abinci baki ɗaya ta yi munin da ba ta yi irin sa haka ba tsawon shekaru bakwai baya.

“Ana samun ƙaruwar ƙarancin abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Gabas, wanda shekaru bakwai da suka gabata ba a fuskanci irin haka ba.

“Domin bayar da gudummawar gaggawa, Gidauniyar UNCERF ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNCRF), ta ware Dala miliyan 11 a matsayin tallafi.

Ya ce wannan gagarimar matsala ce, wadda ke buƙatar kai ɗaukin a cikin gaggawa.

Cikin 2023 dai Hukumar Abinci da Inganta Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa mutum miliyan 31.5 a Najeriya za su fuskanci ƙarancin abinci tsakanin watan Yuni zuwa Agusta, 2024.

People are also reading