Home Back

Gwamnan Kano ya yi alƙawarin gyara titin garin Kundila da ke ƙaramar hukumar Shanono

dalafmkano.com 2024/5/18

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawari gyara titin da ya taso daga babban titin karamar hukumar Shanono zuwa garin Kundila da ke karamar hukumar.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan yayin ta’aziyyar da ya kai na rasuwar ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono Honorable Halilu Ibrahim Kundila.

Marigayin dai ya rasu ne a makon da ya gabata.

Gwamna Abba Kabir Yusif ya kuma bayyana kaɗuwar sa a lokacin da yaji rasuwar Marigayin, inda ya ce mutum ne mai gaskiya da rukon amana.

Wakilinmu na fadar gwamnatin jihar Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Abba Kabir ya kuma ce gwamnatin Jihar Kano za ta dauki nauyin karatun iyalan mamacin daga inda suka tsaya har su kammala karatun nasu.

People are also reading