Home Back

Manyan 'yan takara a zaben Afirka ta Kudu

dw.com 2024/7/5
Südafrika, Johannesburg | ANC-Plakat mit Präsidenten Cyril Ramaphosa
Hoto: James Oatway/REUTERS

Kimanin mutane miliyan 28 ne suka yi tururuwar kada kuri'a a rumfunan zaben kasar Afirka ta Kudu a Larabar nan, a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 30 cif da komawa kan tafarkin dimukuradiyya, bayan fama da mulkin wariyar launin fata daga turawa, cikin yanayin danniya da muzugunawa.

Shugaba mai ci Cyril Ramaphosa na cikin halin tsaka mai wuya, bayan da masana suka yi hasashen cewa ba lallai ne jam'iyyarsa ta ANC ta samu rinjaye a zaben ba, sakamakon taskun da kasar ta fada ciki na kangin rayuwa da fatara da talauci da aikata miyagun laifuka tsakanin al'umma baya ga cin hanci da rashawa da ke zama babban dabaibayin da ke yi wa mulkinsa tarnaki.

To sai dai duk da wannan kalubale jim kadan bayan jefa kuri'arsa Mr Ramaphosa ya bugi kirjin cewa su ke da nasara.

''Wannan kyakkayawar rana ce mai matukar muhimmanci, kuma zabe yana tafiya daidai kamar yadda ya kamata a fadin kasar, hakika na ji dadin zuwa yankin da na girma a ciki, na gaisa da jama'a har da wakilan jam'iyyu da ke rumfar zabe. Kuma ina da kwarin gwiwar cewa al'ummar Afirka ta Kudu za su sake zabar jam'iyyarmu ta ANC''.

Cyril Ramaphosa ya dare kan karagar mulkin ne a shekarar 2018, bayan sauke Jacob Zuma bisa aikata laifuka da suka hada da cin hanci da rashawa, halasta kudaden haram, kin biyan haraji da kuma almundahana.

Mai shekaru 71, Mr Ramaphosa ya yi alkawarin farfado da komadar kasar da ta jima da malkwayewa, ko da yake masharhanta sun ce gazawarsa ta riga ta fito fili karara, sakamakon yadda rashin aiki yi a kasar ya kai kololuwar da ba a taba gani ba a tarihi. Lamarin da ya jefa ANC cikin yanayin fuskantar sakamakon zabe mafi muni.

Shi kuwa jigo a cikin 'yan adawa Julius Malema mai shekaru 43, shi ne jagoran jam'iyyar Economic Freedom Fighters, EFF, wadda ya kafa a shekarar 2013, bayan korarsa da aka yi daga ANC sakamakon tayar da tarzoma, a lokacin yana rike da mukamin shugaban matasa na jam'iyyar. Jam'iyyarsa ta samu karbuwa a kasar sakamakon manufofinta na bunkasa tattalin arzikin kasa da tabbatar adalci da daidaito a rabon filaye ga 'yan kasa. Duk da kallon da ake masa na mai zazzafar siyasa da kuma janyo cece-kuce, Julius Malema na cikin wadanda masu hasashen ke cewa ka iya shugabantar Afirka ta Kudu a nan gaba.

John Steenhuisen na jam'iyyar Democtaric Alliance wato DA, wanda farar fata ne, na daga cikin 'yan takara da ke samun tagomashi a wannan zabe, bayan da ya zama jagoran jam'iyyar a shekarar 2020. haka zalika yana jagorantar hadakar jam'iyyu da ke fatan tankwabar da mulkin daga hannun ANC.

Shi ko tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ta leka ta koma ya gani, bayan da kotun kolin kasar ta soke takararsa, sakamakon tanadin dokar kasar da ya haramta takara ga duk wanda aka taba yankewa hukuncin daurin sama da watanni 12 a kurkuku. Shi ma dai ya yi tattaki zuwa filin zabe domin dangwala kuri'arsa.

Duk da wannan mataki, ana sa ran jam'iyyarsa ta MK za ta tabuka abin kirki a zaben, la'akari da farin jininsa, musamman ma a mahaifarsa ta Kwazulu-Natal. Wanda hakan zai kara janyo wa ANC tazgaro tare da asarar magoya baya.

A nasa jawabin bayan kammala yin zabe, tsohon shugaban kasar Thabo Mbeki, ya ce lokaci ne na sadaukar da kai ga kasa.

Ya ce''Akwai bukatar mu hada kai wuri guda, mu san gudunmawar da za mu bai wa Afirka ta Kudu, wannan abu ne mai matukar muhimmanci. Ya kamata mutane su fito a dama da su a wannan dandali na dimukuradiyya. Ya kamata ANC ta yi abin da ya dace na dawo da Afirka ta Kudu cikin hayyacinta''.

Jam'iyyu 70 da kuma 'yan takara masu zaman kansu 11 ne za su fafata a wannan zabe.))

People are also reading