Home Back

Yajin aikin kwalejojin ilimin Ghana

dw.com 2 days ago
Daliban manyan makarantun Ghana
Daliban manyan makarantun Ghana

A tsarin dokokin makarantun matakin jami'a a Ghana dai, wajibi a rufe su bayan kwashe tsawon ranaki 21 ana yajin aiki mai dorawa sakamakon gurgunta ayyukan ilmantarwa. Kasancewar tuni dai wasu dalibai suka dade a gidajensu, 'yan kalilan da suka rage a makarantu a daya daga cikin kwalejojin ilimin a birnin Accra musamman sabbin shiga ko kuwa ace 100 level ko kuwa level 100 a yadda ake fada a Ghana, sun koka tare da nuna cewa wannan al'amari zai baiwa takwarorinsu a jami'o'i damar yi musu fintinkau kamar yadda wani dalibin ya nuna takaicin halin da suke ciki.

Karin Bayani: Ghana: Barazanar tsadar rayuwa a Ghana

Kokarin jiyo ta bangarorin makarantun dana gwamnati musamman hukumar kwadago NLC da nayi gabanin kammala wannan rahoton ya ci tura. Kana su kansu malaman da ke kasancewa mambobi na kungiyar CETAG na cewa wannan al'amari ba dadinsa suke ji ba domin yana komawa da aikinsu baya. Tun a makon jiya ne dai hukumar kwadagon NLC ta bukaci CETAG ta dakatar da yajin amma tayi mata birris, wanda hakan ya sanya NLC kai wa ga matakin daukaka kungiyar CETAG kara kotu. Abin zaman jira a gani shi ne yadda zata kaya tare da sa ran cewa gwamnati ba za ta jira har I kaiwa ga matakin rufe makarantun ilimi a kasar ba.

People are also reading