Home Back

EFCC ta yi nasarar hukunta mutum 3,175 a kotu, ta ƙwato Naira biliyan 156 cikin shekara ɗaya – Olukoyede, Shugaban EFCC

premiumtimesng.com 2024/7/5
Kotu ta kwato maka-makan gidaje 48 a hannun tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF
EFCC Officials

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya bayyana cewa hukumar sa ta yi nasara kan ƙararraki 3,175 na mutanen da ta gurfanar kuma aka yanke masu hukunci baban-daban a kotunan ƙasar nan, a cikin shekara ɗaya

Haka kuma ya ƙara da cewa duk a cikin shekara ɗayar dai, EFCC ta ƙwato zunzurutun Naira biliyan 156 da miliyan 276 cikin shekara ɗaya, daga ranar 29 ga Mayu 2023, zuwa ranar 29 ga Mayu 2024.

Ya bayyana hakan a ranar Laraba, 29 ga Mayu, lokacin da yake jawabi wurin taron ‘Zero Tolerance Club’, a Jami’ar Abuja, wadda ke Gwagwalada, Abuja.

Olukoyede wanda ya yi jawabi ta bakin sakataren EFCC, Mohammed Hammajoda, ya ce EFCC ta kuma ƙwato Dala miliyan 43. 835. Sai Fam na Ingila 25,365.00. Wasu fam 286,847, sai fam 51,360, sai Yuro 74,754, Riyal 35,000 da kuma Dirhami 42,390. Sai kuma kuɗin ‘yan kirifro har 867831.

Da ya ke ƙarin bayani, ya ce duk da EFCC ta yi hoɓɓasa sosai a farkon shekarar, ƙasa samun fantsamar matasa cikin harƙallar intanet da zamba ya na ƙara zama abin damuwa ga jami’an yaƙi da cin hanci da rashawa.

Daga nan ya yi kira ga ɗaliban jami’ar su nesanci harƙalla da zamba a intanet, ya kuma jaddada cewa “hukuncin ɗaurin laifin zamba mummunan tabo ne wanda ba ya warkewa a jikin matasa.”

Daraktan Sanarwa da Yaɗa Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren ya ce sun je jami’ar ce domin buɗe ƙaddamar da ‘Zero Tolerance Club’ kuna ai yawo hankalin matasa domin su nesanci Illolin cin hanci da rashawa.

Sai dai shugaban na EFCC ban fayyace adadin nawa daga cikin kuɗaɗen aka ƙwato daga hannun ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati ba.

People are also reading