Home Back

Kasashen Sahel biyar na atisayen soji a Jamhuriyar Nijar

dw.com 2024/7/1
Sojojin Burkina Faso da na Niger a lokacin da suka karbar horon hadin gwiwa daga sojojin Amurka
Sojojin Burkina Faso da na Niger a lokacin da suka karbar horon hadin gwiwa daga sojojin Amurka

Nijar wacce ke karbar bakuncin itisayen a yankin Tillaa, ta ce kasashen yankin Sahel din da suka shiga shirin sun hada da Burkina Faso da Chad da Mali da Togo sai kuma Nijar mai masaukin baki.

Uku daga cikin kasashen Burkina Faso da Nijar da kuma Mali da suka hambarar da gwamnatocin farar hula sun fatattaki dakarun Faransa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen, da zummar ci gaba da daukar ragamar yaki da 'yan ta'adda a shiyyar tare da maida hankali kan neman goyon bayan kasar Rasha.

Kutsen sojoji a gwamnatocin kasashen ya sake haifar da matsalar tsaro da rudanin siyasa da bukatar kayan agajin jinkai a kasashen uku.

People are also reading