Home Back

Rigima Ta Ƙara Tsananta, APC Ta Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci a Jiha 1

legit.ng 2024/7/3

Jihar Rivers - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) reshen jihar Ribas ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar da jam'iyyar PDP kemulki.

Jam'iyyar APC ta buƙaci shugaban kasa ya ya ɗauki wannan matakin ne saboda rikicin da ya ɓarke a jihar Ribas bayan karewar wa'adin shugabannin ƙananan hukumomi.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta jihar, Tony Okocha ya ce matakin zai daƙile kashe-kashen rayuka da kuma kawo ƙarshen rikicin da ke ƙara tsananta.

Wannan kira na APC na zuwa ne jim kaɗan bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya rantsar da kantomomi 23 ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, cewar The Nation.

Idan baku manta ba Gwamna Fubara ya maye gurbin shugabannin ƙananan hukumomin da ke goyon bayan ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Kashi na karko na kantomomi 11 watau shugabannin kananan hukumomi na riƙon kwarya sun karɓi rantsuwar kama aiki a fadar gwamnatin Ribas yau Laraba.

Ku saurari ƙarin bayani...

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

People are also reading